Zanga Zanga Ta Barke a Majalisa, an Bukaci Tinubu Ya Dauki Mataki kan Mele Kyari

Zanga Zanga Ta Barke a Majalisa, an Bukaci Tinubu Ya Dauki Mataki kan Mele Kyari

  • Gungun masu zanga-zanga sun durfafi Majalisar Tarayya domin bukatar a kori shugaban kamfanin NNPCL, Mele Kyari
  • Matasan da ke wakiltar kungiyoyi sun bukaci Bola Tinubu ya gargadi Kyari kan tsare-tsare da za su jefa al'umma cikin kunci
  • Hakan na zuwa ne yayin da ake zargin kamfanin da kaso tsare-tsare da ke sake jefa yan Najeriya cikin mawuyacin hali

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - Masu zanga-zanga sun fantsama kusa da Majalisar Tarayya da ke birnin Tarayya Abuja.

Masu zanga-zangar sun bukaci a yi bincike kan shugaban NNPCL, Mele Kyari kan kawo cikas a harkokin mai.

An bukaci Tinubu ya sallami Mele Kyari daga shugabancin NNPCL
Masu zanga-zanga sun roki Bola Tinubu ya kori shugaban NNPCL, Mele Kyari. Hoto: Asiwaju Bola Tinubu, NNPC Limited.
Asali: Twitter

An roki Tinubu ya kori Mele Kyari

Kara karanta wannan

Sabuwar matsala ta afkawa Ganduje kan bidiyon dala, an tono wasu zarge zarge

Punch ta ce kungiyoyin da suke zanga-zangar suka ce Kyari bai tsinana komai ba wurin inganta ɓangaren mai a ƙasar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Zanga-zangar da aka yi ta a kusa da Majalisar Tarayya da dauki hankulan al'umma da ke kewayen, The Guardian ta ruwaito.

Mai magana da yawun kungiyar, Segun Adebayo ya bukaci Bola Tinubu ya gargadi Kyari kan kawo tsare-tsare da za su jefa al'umma cikin kunci.

Korafe-korafen da ake yi kan Mele Kyari

"Duk da yiwuwar tace mai daga matatunmu na gida, wasu sun gwammace a cigaba da shigo da mai daga ketare domin biyan buƙatarsu."
"Shigo da mai din ba karamin asarar daloli ke jawowa ba wanda daga bisani ke komawa kan talakawa yayin da tsiraru ne ke cin gajiyar."
"Akwai wadanda ke fifita abin da za su samu fiye da cigaban ƙasa, irinsu ke kawo cikas ga samun cigaba a Najeriya."

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun sake kai mummunan hari, sun kashe bayin Allah ta hanya mai muni

- Segun Adebayo

Zanga-zanga ta barke a hedikwatar NNPCL

Kun ji cewa masu zanga-zanga sun cika hedikwatar kamfanin NNPCL a Abuja inda suka bukaci kawo sauyi tattare da harkokin mai.

Matasan da ke zanga-zangar sun bukaci Mele Kyari ya yi gaggawar ajiye aikinsa na shugaban kamfanin NNPCL saboda gazawa.

Hakan ya biyo bayan korafe-korafe kan tashin farashi da yawan layi da ake samu a gidajen mai da kuma halin kunci da aka shiga.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.