'Zargin Cin Zarafi': Direban Tasi Ya Yi Amai Ya Lashe, Ya ba Dan Majalisa Hakuri

'Zargin Cin Zarafi': Direban Tasi Ya Yi Amai Ya Lashe, Ya ba Dan Majalisa Hakuri

  • Direba a Abuja, Stephen Abuwatseya, ya nemi afuwar dan majalisar Abia, Alex Ikwechegh, kan rigimar da ta shiga tsakaninsu
  • Cin zarafin da aka yi wa direban ya jawo ce-ce-ku-ce, inda aka fara kiran a tsige dan majalisar kan yiwa direban motar barazana
  • Wasu 'yan Najeriya sun yi martani mai zafi bayan direban ya ba da hakuri, inda suka yi zargin an tursasa shi ko an ba shi cin hanci

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Abuja - A wani abin mamaki, direban Bolt mazaunin Abuja, Stephen Abuwatseya, ya nemi afuwar dan majalisar wakilai na jihar Abia, Hon. Alex Mascot Ikwechegh.

An rahoto cewa Alex Ikwechegh, wakilin mazabar Aba ta Arewa da Kudu a majalisar wakilai, ya zabgawa direban mari kan wata 'yar hatsaniya da ta afku tsakaninsu.

Kara karanta wannan

'Ban tsoron EFCC': Gwamnan PDP ya bugi kirji, ya fadi abin da zai yi idan suka neme shi

Direban tasi da dan majalisa ya yiwa barazana ya fito ya ba da hakuri
Direban tasi a Abuja ya ba dan majalisar Abia, Ikwechegh hakuri. Hoto: Alex Ikwechegh/Stephen Abuwatseya
Asali: Facebook

Direba ya nemi afuwar ɗan majalisa

Kwanaki bayan afkuwar lamarin, an ga direban a cikin wani bidiyo yana nuna nadama kan rawar da ya taka a rigimar, inda ya ce halayensa sun tunzura dan majalisar har ya ci zarafinsa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Direban motar ya kuma nemi gafarar 'yan Najeriya inda ya nemi a samu hadin kai.

Direban ya ce:

"Barkanku, 'yan Najeriya, na samu rashin fahimta da Hon. Alex Mascot Ikwechegh kwanan nan."
"Ina son neman afuwa gare shi kan duk abin da na faɗa ko na yi da ya harzukashi har ya yi fusata haka."

Direban ya kuma yi kira ga jama’a da su manta da abin da ya faru, su mai da hankali kan hadin kai, inda ya kara da cewa:

“Lokaci bai yi ba da za mu fara samun rabuwar kawuna a kan addini, kabila, ko yanki ba.

Kara karanta wannan

Mutane miliyan 33 za su kamu da yunwa a 2025, an fadi jihohin da abin zai shafa

“A gaskiya ya kamata mu hada kai, mu ga yadda za mu hada kan wannan al’umma, mu ciyar da ita gaba."

Duba bidiyon nan:

Ƴan Najeriya sun yi martani

Uzurin da direban ya bayar ya janyo ce-ce-ku-ce mai yawa yayin da ƴan Najeriya suka tofa albarkacin bakinsu a kafafen sada zumunta

@flourish007 ya ce:

"Lokacin da wanda aka zalunta ya kare wanda ya zaluncesa saboda karfin iko, yana nuna cewa ba abin da ‘yan siyasar mu ba za su iya aikatawa ba. Sun saye shi.

@ChuksEricE ya ce:

"Abin takaici ne sosai 🤦"

@Statesman1010 ya ce:

"Komai zai iya faruwa a Najeriya... a bayyana yake cewa ko dai an yi wa mutumin barazana ko kuma an yi masa wani tayin kudi."

@Dgoldboss ya ce:

"Ɗaya daga cikin dalilan da ya sa taimaka wa ‘yan Najeriya yake da wahala. Suna haduwa da daidai irinsu kusan kowane lokaci."

'Dan majalisar Abia ya nemi yafiyar jama'a

Kara karanta wannan

Janar Lagbaja na cigaba da jinya, Tinubu ya karawa mukaddashin hafsan sojoji girma

A wani labarin, mun ruwaito cewa dan majalisar wakilai na jihar Abia, Hon. Alex Mascot Ikwechegh ya nemi afuwar jama'a bayan korafin jama'a kan cin zarafin direba.

Yayin da ce-ce-ku-ce ya yawaita kan abin da dan majalisar ya aikata, Hon. Alex Ikwechegh ya ce ya yi nadamar aikata abin, ya bukaci yafiya daga al'umma.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.