'Babu Laifi': Lauyan Tinubu Ya Sake Magana kan Yaran da Aka Kama, Ya Fadi Tsarin Doka
- Bayan sakin yara ƙanana da aka garkame a Abuja, Ministan Shari'a ya sake kare matakin Gwamnatin Tarayya na cafke su
- Lateef Fagbemi SAN ya ce babu inda dokar Najeriya ta haramta hukunta yara idan har suka saba ka'ida a kasar
- Lateef Fagbemi SANya ce babu inda dokar Najeriya ta haramta hukunta yara idan har suka saba ka'ida a kasara
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
FCT, Abuja - Ministan shari'a a Najeriya, Lateef Fagbemi ya sake magana kan tsare yara 72 da aka yi a Abuja.
Lateef Fagbemi ya ce a doka babu inda aka ce kada a gurfanar da yara ƙanana idan suka yi laifi ko saba dokar kasa.
Gwamnatin Tinubu ta kare tsare kananan yara
Vanguard ta ruwaito cewa Fagbemi ya tabbatar da haka ne a ranar Alhamis 7 ga watan Nuwambar 2024.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Yayin bayaninsa, Fagbemi ya ce duk abin da ya faru da kama yaran da aka yi duka an yi ne karkashin dokar kasa.
Babban Lauyan ya tabbatar da cewa babu wani wuri a cikin dokokin Najeriya da ya haramta hukunta yara.
"Babu wata doka a Najeriya da ta haramta hukunta yara idan suka yi laifi a kasa."
"Na ji wasu ma suna ba da shawara cewa ya kamata a kai yaran kotun iyali."
- Lateef Fagbemi SAN
Ministan shari'a ya yabawa Tinubu kan sakin yara
Ministan ya ce laifin babba ne, sai ya yabawa matakin Bola Tinubu na umarnin sake yaran daga kulle bayan surutu da aka yi a cewar TheCable.
Fagbemi ya ce Tinubu ya nuna tausayawa da ya umarci sakin yaran wanda ya kwantar da hankula a fadin kasa baki daya.
Gwamna ya gwangwaje yara 32 da aka sake
Kun ji cewa Gwamnatin jihar Kaduna ta shirya tallafawa yaran da gwamnatin Bola Tinubu ta sako kan zargin shiga zanga-zanga Sanata.
Mai girma Uba Sani ya karbi bakuncin yaran inda ya yi wa kowane daya kyautar N100,000 da kuma sabuwar babbar waya.
Uba Sani ya kuma yi alkawarin samar musu ayyukan yi tare da ba wasu daga cikinsu jari domin tsayawa da kafafunsu.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng