Abba Ya Gabatar da Kasafin N549bn, An Gano Inda Zai fi Kashe Kudi a 2025

Abba Ya Gabatar da Kasafin N549bn, An Gano Inda Zai fi Kashe Kudi a 2025

  • Rahotanni sun nuna cewa gwamna Abba Kabir Yusuf gabatar da kasafin kudin shekarar 2025 a gaban majalisar dokokin jihar Kano
  • A kasafin kudin Kano na 2025, Abba Kabir Yusuf ya fifita bangaren ilimi da kaso mafi tsoka inda ya ce hakan zai kawo cigaba a jihar
  • Shugaban majalisar dokokin jihar Kano, Jibril Isma'il Falgore ya tabbatarwa gwamnan cewa za su yi nazari kan kasafin da gaggawa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Kano - Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf ya gabatar da kasafin kudin N549bn na shekarar 2025 ga majalisar dokokin jihar.

Bangarorin ilimi, kiwon lafiya da noma na cikin wuraren da gwamnan zai mayar da hankali a kai a 2025 kasancewar sun samu kaso mafi tsoka.

Kara karanta wannan

Jerin kasashen Afrika 5 da suka fi bata lokaci a kafofin sadarwa ta zamani

Abba Kabir
Abba ya gabatar da kasafin kudin 2025. Hoto: Abba Kabir Yusuf
Asali: Facebook

Legit ta tattaro bayanai kan yadda gwamnan ya gabatar da kasafin ne a cikin wani sako da ya wallafa a Facebook.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

N549b: Abba ya gabatar da kasafin 2025

Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf ya gabatar da kasafin kudin shekarar 2025 a gaban majalisar dokokin jihar.

Abba Kabir Yusuf ya bukaci majalisar ta amince da N549bn a matsayin kasafin kudin Kano na 2025 wanda ya haura kasafin 2024 da N111.8bn.

Bangarorin da suka samu kaso mai tsoka a Kano

Bangaren ilimi ya samu kaso mafi tsoka inda aka ware masa N168.5bn wanda ya kai kashi 31% na dukkan kasafin kudin.

Bangaren lafiya na Kano ya kwashi kaso 16% na kasafin kudin 2025, an ware masa kudi har N90bn a badi.

Bangaren noma ya samu kaso 3.8% na kasafin kudin Kano na shekarar 2025 watau an ware masa N21bn.

Kara karanta wannan

Likitoci sun gana da gwamnan Kano, sun canza matsaya kan shiga yajin aiki

Alfanun kasafin kudin Kano na 2025

Abba Kabir Yusuf ya bayyana cewa yana da tabbacin cewa kasafin kudin zai zamo sila na magance matsalolin jihar kuma zai yi kokarin aiwatar da shi baki daya.

Shugaban majalisar dokokin jihar Kano, Jibril Isma'il Falgore ya tabbatarwa gwamnan cewa za su kammala nazarin kasafin kudin cikin kankanin lokaci.

Majalisar Kano ta magantu kan rikicin NNPP

A wani rahoton, kun ji cewa majalisar dokokin jihar Kano ta yi bayani kan cewa yan NNPP sun rabu gida biyu saboda fitowar salon 'Abba tsaya da kafarka'

Shugaban masu rinjaye a majalisar, Hon. Lawan Hussaini ya yi bayani filla filla kan hakikanin abin da ke faruwa a kwanan nan a NNPP.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng