An Sake Zabar dan Najeriya a Matsayin dan Majalisar Dokokin Amurka
- Amurkawa a yankin Columbia District (DC) sun sake zabar dan asalin Najeriya ya kare ra'ayinsu a majalisar dokokin kasar
- An zabi Oye Owolewa a karo na biyu inda zai taka rawa wajen ganin ba a tauye yankin da ya ke wakilta ba
- An zabi Owolewa a matsayin 'shadow representative' wanda ba su da ikon zabe a majalisar dokokin Amurka
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad: A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Kasar America - Dan asalin Najeriya da ke jam'iyyar Democrat a Amurka, Oye Owolewa ya sake yin nasarar zama wakilin ra'ayin mutanen gundumar Columbia (DC) a majalisar dokokin Amurka. Oye Owolewa ya kafa tarihi bayan ya zama dan asalin Najeriya na farko da aka zaba a majalisar a shekarar 2020.
Jaridar The Cable ta duk da gwamnatin Amurka ba za ta saurari dan majalisar a hukumance ba, amma zai rika kare bukatun gundumarsa a kokarinta na zama jiha.
Owolewa ya godewa Amurkawa bayan zabar sa
A sakon da ya wallafa a shafinsa na X, Oye Owolewa ya godewa Amurkawa da su ka zazzaga masa kuri'a har ya yi nasarar komawa majalisar dokokin Amurka.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Oyo Owolewa ya yi nasara a zaben da kuri'a 164,026 wanda ya yi dai-dai da 82.84% na kuri'un da aka kada a zaben.
Aikin yan majalisar Amurka irinsu Owolewa
Ana zabar yan majalisa marasa karfin ikon kada kuri'a a majalisar dokokin Amurka da ake kira 'shadow representatives' domin kare bukatun yankunansu.
Bayan sake zabarsa da aka yi, Oye Owolewa ya yi godiya ga kamfanoni da daidaikun mutanen da su ka taimaka ya kai ga nasara sake komawa kujerarsa.
Zaben Amurka: An fadi wanda ya yi nasara
A wani labarin kun ji cewa an fadi wanda ya yi nasara a zaben shugaban kasar Amurka tsakanin tsohon shugaba, Donald Trump da mataimakiyar shugaban kasa, Kamala Haris.
A ranar Talata, 5 ga Nuwamba ne aka kada kuri'u a kasar Amurka, inda Donald Trump ya ka da abokiyar takararsa, kuma zai zama shugaban Amurka na 47 a tarihin kasar.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng