An Kama Riƙakƙun Yan Fashi da Makami, Sun Sace Kayan Miliyoyi

An Kama Riƙakƙun Yan Fashi da Makami, Sun Sace Kayan Miliyoyi

  • Rundunar yan sanda a jihar Edo ta tabbatar da kama wasu mutane hudu da ake zargi sun yi fashi da makami a gidan wani mutum
  • Bayanan yan sanda sun tabbatar da cewa an yi fashi da makamin ne a Ibie ta Kudu a karamar hukumar Etsako ta Yamma a Edo
  • Kwamishinan yan sandan jihar Edo, CP Umoru Ozigi ya yi karin haske kan yadda jami'an tsaro suka cafke wadanda ake zargin

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Edo - Jami'an yan sanda sun cafke wasu mutane hudu da ake zargi da fashi da makami.

Rahotanni sun tabbatar da cewa kama daya daga cikin yan fashi da makamin da ake zargi ne ya jawo tonuwar asirin sauran yan uwansa.

Kara karanta wannan

Ire iren ta'addancin da sabuwar kungiyar Lakurawa ke yi a Arewa

Yan sanda
An kama yan fashi a Edo. Hoto: Nigerian Police Force
Asali: Facebook

Jaridar Daily Trust ta wallafa cewa kwamishinan yan sandan jihar Edo, CP Umoru Ozigi ya tabbatar da cafke wadanda ake zargin.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda aka yi fashi a jihar Edo

Kwamishinan yan sanda, CP Umoru Ozigi ya bayyana cewa wani mutum mai suna Daramola Gabriel ya kai kara caji ofis kan fashi da aka yi masa.

Daramola Gabriel ya fadawa yan sanda cewa wasu yan fashi sun shiga masa gida sun wawushe masa kayan miliyoyin Naira.

Yan fashin, dauke da manyan makamai sun shiga gidan Gabriel ne da ke bayan wani hotel a karamar hukumar Etsako.

An kama riƙakƙun yan fashi da makami

Wata rana Gabriel zai shiga mota a tasha sai ya kalli wani matashi sanye da dan kunnensa na zinare da aka sace yayin fashin.

Nan-take ya sanar da yan sanda kuma suna zuwa suka kama matashin wanda daga bisani ya nuna sauran mutane uku da ake zargi sun yi fashi tare.

Kara karanta wannan

Yan bindiga sun sace limami da mutane sama da 100 a Zamfara

'Yan fashin da aka kama a Edo

CP Umoru Ozigi ya bayyana cewa cikin wadanda aka kama da zargin sun hada da Osakpolor Edobor dan shekaru 20.

Haka zalika akwai Oshoike Malik mai shekaru 23, Aliu Rabak mai shekaru 27 sai kuma Alor Ojo mai shekaru 24 da haihuwa.

An kama yan fashi a Jigawa

A wani rahoton, kun ji cewa rundunar yan sanda a Jigawa ta samu nasara kan tarin yan fashi a ƙananan hukumomin jihar daban daban.

Bayan sata, wasu daga cikin yan fashin da aka kama ana zargin sun yi barazanar kisa ga mutane da dama a yankunan jihar Jigawa.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng