Sabuwar Matsala Ta Afkawa Ganduje kan Bidiyon Dala, an Tono Wasu Zarge Zarge
- Shugaban jam'iyyar APC, Abdullahi Ganduje ya shiga wata matsala bayan an bukaci EFCC ta cafke shi kan cin hanci
- Kungiyoyin yaki da cin hanci sun shigar da korafi kan EFCC domin daukar mataki kan tsohon gwamnan Kano game da zarge-zargen
- Hakan na zuwa ne yayin da ake zargin Ganduje da badakalar makudan kudi lokacin da yake mulkin Kano daga 2015 zuwa 2023
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
FCT, Abuja - Kungiyoyin yaki da cin hanci a Najeriya sun shigar da korafi kan hukumar EFCC.
Kungiyoyin sun bukaci hukumar ta cafke tare da hukunta shugaban jam'iyyar APC, Abdullahi Ganduje.
An bukaci hukumar EFCC su cafke Ganduje
Leadership ta ce kungiyoyin guda 51 suna zargin tsohon gwamnan da almundahana da dukiyar al'umma.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kungiyoyin sun shigar da korafin ne kan EFCC a ranar Alhamis 7 ga watan Nuwambar 2024 da muke ciki.
Suna zargin Dakta Ganduje kan cin hanci da rashawa lokacin da yake mulkin Kano daga shekarar 2015 zuwa 2023.
Kakakin kungiyar NACA, Kwamred Umar Ideresu ya ce zarge-zargen sun cancanci a kama shi.
Kungiyoyi sun sake bankado badakalar Ganduje
"Akwai takardu da shaidu da ke nuna cin hanci na Ganduje karara, a 2018, Daily Nigerian ta wallafa wani faifan bidiyo da ke nuna Ganduje ya na karbar cin hancin $5m daga yan kwangila."
"A 2023, hukumar yaki da cin hanci a Kano ta gayyaci Ganduje amma bai amsa gayyatar ba."
"NACA ta bukaci EFCC ta dauki matakin cafke shi da kuma hukunta shi kan badakalar N57.43bn."
- Cewar sanarwar
Kungiyar har ila yau, ta bukaci hukumar ta tabbatar da gaskiya da gudanar da aikinta cikin gaskiya, cewar BusinessDay.
Kotu ta yi zama kan shari'ar Ganduje
Kun ji cewa babbar kotu da ke zamanta a birnin Tarayya Abuja ta kara kwanaki kafin yanke hukunci kan karar da ke neman a kori Abdullahi Ganduje.
Jagora a APC da ya fito daga Arewa ta Tsakiya, Saleh Zazzaga na ganin bai da ce Dr. Ganduje ya jagoranci jam'iyyar ba saboda yankin da ya fito.
Zazzaga ya ce mukamin shugabancin APC a yanzu ya fada shiyyarsu, wanda hakan ya sa su mika damuwarsu zuwa babbar kotun tarayya.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng