Gwamnatin Tinubu Ta Fadi Yadda Ta ke Fitar da Matasa daga Talauci

Gwamnatin Tinubu Ta Fadi Yadda Ta ke Fitar da Matasa daga Talauci

  • Gwamnatin tarayya ta ce ta na sane da matasan kasar nan kuma za ta fitar da su daga talaucin da ya dame su a yau
  • Sakataren gwamnati, George Akume ne ya fadi haka a taron raba kayan aiki ga matasan da aka koyawa sana'o'i
  • Ya ce ta cikin shirin, gwamnati za ta horar da matasa 5,000 da za a fara a jihohi uku, wanda aka soma da jihar Neja

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Benue - Duk da tarin matsalolin da matasa ke kokawa da su, Sakataren gwamnatin tarayya, George Akume ya ce akwai wasu tsare-tsare a kasa.

Kara karanta wannan

Gwamnati ta dauko aiki, mata za su fara haihuwa kyauta a asibiti a Najeriya

Sanata George Akume ya ce gwamnatin Bola Tinubu ta na da niyyar ganin an samu wadata a tsakanin yan Najeriya, daga ciki har da matasa

Tinubu
Gwamnati ta fadi shirinta kan matasa Hoto: Bayo Onanuga
Asali: Facebook

Jaridar Punch ta wallafa cewa George Akume ya fadi haka ne a taron raba kayan aiki ga matasa 689 da aka yaye daga shirin samar da wutar lantarki ta hanyar ruwa da hadin gwiwar hukumar cigaban matasa a Binuwai.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamnatin Tinubu na shirin koyawa matasa sana'o'i

Sakataren gwamnatin Najeriya, George Akume ya bayyana cewa akwai shiri a kasa da gwamnati ke aiwatarwa, ciki har da shirin koyar da matasa sana’o’i.

Sanata Akume wanda ya samu wakilcin shugaban ma’aikatansa, Simeon Tyungu, ya ce shirin da aka yi a Binuwai, za a aiwatar da su a wasu jihohi shida.

Gwamnatin tarayya na shirin taimakon matasa

Saboda yawan matasan ƙasar nan, Sakataren gwamnati ya ce su 5,000 aka zakulo a wannan shirin da gwamnati ta bijiro da shi.

Kara karanta wannan

Zanga zanga: Kashim Shettima zai tarbi yara bayan gwamnati ta janye shari'a a kotu

Ya ce an fara shirin a Neja da ke jihar Minna, sannan an raba wasu kayayyakin a jihar Filato an kuma yi makamancinsa a Binuwai..

Matasa sun mika bukata ga gwamnatin Tinubu

A baya mun ruwaito cewa matasan Najeriya sun fusata da yadda rashin wuta ya zama ruwan dare, kuma har yanzu gwamnatin tarayya ta gaza magance matsalar.

A wata hira da mazauna Arewacin Najeriya, sun mika bukata ga shugaba Bola Ahmed Tinubu na gaggauta daukar matakin da zai kawo ƙarshen matsalar wutar lantarki.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.