Mutane Miliyan 33 Za Su Kamu da Yunwa a 2025, An Fadi Jihohin da Abin Zai Shafa
- Rahoton da Cadre Harmonisé ta fitar ya nuna cewa akalla 'yan ajeriya miliyan 33.1 za su fuskanci karancin abinci a 2025
- Majalisar Dinkin Duniya, shirin samar da abinci na duniya, ma’aikatar noma da samar da abinci ta Najeriya suka yi binciken
- Rahoton ya bayyana abin da zai jawo matsananciyar yunwa a jihohi 26 da Abuja a 2025 tare da miliyoyin yara, mata da zai shafa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Abuja - Rahoton Cadre Harmonisé na watan Oktoba ya yi hasashen cewa aƙalla 'yan Najeriya miliyan 133.1 za su fuskanci matsalar abinci a shekarar 2025.
Rahoton ya nuna cewa yunwa za ta kama miliyoyin 'yan Najeriya daga jihohi 26 da babban birnin tarrayya Abuja tsakanin Yuni da Agustan badi.
Wannan hasashen ya fito ne daga cikin rahoton nazari na cibiyar CH da aka fitar ranar Juma’a a Abuja, a cewar jaridar Punch.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Jihohin da yunwa za ta shafa a 2025
Hukumar kula da abinci da noma ta Majalisar Dinkin Duniya, shirin samar da abinci na duniya, ma’aikatar noma da samar da abinci ta tarayya da wasu abokan hulda ne suka gudanar da binciken.
Jihohin da abin yunwa za ta shafa sun hada da Sokoto, Zamfara, Borno, Adamawa, Yobe, Gombe, Taraba, Katsina, Jigawa, Kano, Bauchi, Filato, Kaduna, Kebbi, Neja da Benuwai.
Sauran jihohin da abin zai shafa sun hada da Cross River, Enugu, Edo, Abia, Kogi, Nasarawa, Kwara, Ogun, Lagos, Rivers, da kuma babban birnin tarayya Abuja.
Miliyoyin mutane za su rasa abinci
A cewar rahoton Vanguard, binciken Cadre Harmonisé ya nuna cewa mutane miliyan 33.1 za su fuskanci matsanancin karancin abinci a tsakanin Yuni da Agustan 2025.
Adadin wanda ya haura da mutane miliyan bakwai idan aka kwatanta da na shekarar 2024, ya karu ne saboda tsadar abinci, sauyin yanayi da tashe tashen hankula a Arewa.
Rahoton ya yi gargadin cewa yunwa za ta kama yara miliyan 5.4 da mata 800,000 masu juna biyu da masu shayarwa daga jihohin Borno, Adamawa, Yobe, Sokoto, Katsina, da Zamfara.
Matsalar karancin abinci a Najeriya
A wani labarin, mun ruwaito cewa kungiyar abinci da noma (FAO) ta Majalisar Dinkin Duniya ta gudanar da bincike mai zurfi kan matsalar yunwa da ta addabi Najeriya.
Binciken ya nuna cewa koma bayan tattalin arziki, ambaliyar ruwa, rikici, matsalar tsaro na cikin abubuwan da suka taka rawa wajen rashin wadatar abinci a Najeriya.
Asali: Legit.ng