'Yan Bindiga Sun Sake Kai Mummunan Hari, Sun Kashe Bayin Allah Ta Hanya Mai Muni
- Wasu mahara da ake zaton ƴan bindiga ne sun hallaka matasa uku tare da raunata wasu mutum biyu a jihar Filato
- Kungiyar matasan Berom ta tabbatar da faruwar lamarin, ta ce sha'anin tsaro na kara taɓarɓarewa a yankin nasu
- Ta buƙaci jami'an tsaro musamman rundunar Operation Safe Haven su tashi tsaye wajen maganin waɗannan tsageru
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Plateau - Wasu mahara sun kashe matasa uku tare da jikkata wasu a kauyen Rakok da ke karamar hukumar Barkin-Ladi a jihar Filato a ranar Laraba.
Ƙungiyar matasan Berom ta bayyana cewa ƴan bindigar sun yi wa matasan kisan wulaƙanci a harin da suka kai garin ba zato ba tsammani.
Hakan na ƙunshe ne a wata sanarwa mai ɗauke da sa hannun shugaban ƙungiyar matasan, Dalyop Mwantiri, kamar yadda Channels tv ta ruwaito.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Yadda ƴan bindiga suka kashe matasa 3
Ya ce matasan na tsaka da gudanar da harkokinsu na yau da kullum, kwatsam maharan suka shigo kauyen suka masu kisan gilla.
Kungiyar ta yi Allah wadai da wannan sabon harin, inda ta yi kira ga hukumomin tsaro su tashi tsaye su dakatar da lamarin da ma lalata amfanin gonakin da ake yi.
Sanarwar ta ce:
"Ya kamata a ɗauki matakin soji domin dakile kashe-kashe, cin zarafin mata da lalata amfanin gona kamar masara mallakin ƴan kabilar Berom tun kafin abin ya yi muni.
Don haka ƙungiyar matasan Berom BYM na kira ga jami'an tsaro musamman sojojin rundunar Operation Save Haven su gaggauta kawo ƙarshen wannan zubar da jini."
Matasa sun bukaci gwamnati ta biya diyya
Kungiyar ta nemi mahukunta su sa a gudanar da bincike tare da kama wadanda suke kashe-kashe da kuma biyan diyyar dimbin amfanin gonakin da aka lalata ma jama'a.
Har yanzu rundunar ‘yan sanda da rundunar hadin gwiwa ta Operation Safe Heaven ba su fitar da wata sanarwa a hukumance kan harin ba.
Sojoji sun kashe jagoran ƴan bindiga a Filato
A wani rahoton, an ji cewa dakarun soji a karamar hukumar Wase da ke jihar Filato, sun kashe yan bindiga biyar, ciki har da shugabansu, Kachalla Saleh.
Kashe Kachalla Saleh na zuwa ne kasa da mako guda bayan wata arangama tsakanin ‘yan bindiga da ’yan banga a yankin.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng