'Wa'adi Ya Kare': Likitoci Sun Tsunduma Yajin Aiki a Jihar Kano, Bayanai Sun Fito
- Likitoci da ke aiki a asibitin Murtala Muhammad da ke cikin jihar Kano sun sanar da shiga yajin aikin sai baba ta gani
- A karkashin kungiyar likitocin Najeriya (NMA) sun ce shiga yajin aikin ya zama tilas saboda cin zarafin abokiyar aikinsu
- Legit Hausa ta ce likitocin sun ba gwamnatin Kano wa'adin awanni 48 na korar kwamishiniyar ma'aikatar jin kai
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Kano - Wa'adin awanni 48 da kungiyar likitocin Najeriya (NMA) ta debawa gwamnatin jihar Kano ya kare ba tare da an biya bukatun da ta gabatar ba.
Bayan karewar wa'adin, kungiyar likitocin ta sanar da janye ayyukanta daga asibitin kwararru na Murtala Muhammad da ke cikin jihar.
Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa tsunduma yajin aikin na da alaka da cin zarafin da kungiyar ta yi zargin an yiwa wata likita a sashen masu juna biyu asibitin.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Likitoci sun shiga yajin aiki a Kano
A cewar jami’in hulda da jama’a na NMA a Kano, Dakta Muhammad Aminu Musa, shiga yajin aikin ya biyo bayan halin ko in kula da gwamnatin Kano ta nuna kan lamarin.
Dakta Muhammad ya ce:
"Wani bincike da ma’aikatar lafiya ta gudanar ya tabbatar da cewa likitar ba ta da laifi, inda ya tabbatar da cewa ta yi aiki da cikakkiyar kwarewa a aikinta.
“Duk da haka, babu wani mataki da aka dauka don magance rashin da’a na kwamishiniyar ma’aikatar jin kai, wadda ta ci zarafin likitar a bakin aikinta."
Kano: Likitoci sun ba gwamnati sharadi
Don haka kungiyar NMA a Kano ta janye dukkan ayyukan jinya a asibitin kwararru na Murtala Muhammad daga karfe 12 na ranar 6 ga watan Nuwamba 2024.
Sanarwar ta ce kungiyar ba za ta janye yajin aikin ba har sai gwamnati ta kori kwamishiniyar tare da samar da isassun ma’aikata da rabon kayan aiki da kuma inganta matakan tsaro.
"Ya zama wajibi gwamnatin Kano ta dauki matakai na samar da isassun likitoci a asibitin, a tabbatar likitoci ba sa aiki karkashin su ko yanayin da ke barazana ga lafiyarsu."
- A cewar Dakta Muhammad.
Likitoci sun ba Abba wa'adin awanni
Tun da fari, mun ruwaito cewa lungiyar likitoci ta NMA, reshen Kano ta ba gwamnatin jihar wa'adin awanni 48 ta kori kwamishiniyar jin kai, Hajiya Amina Abdullahi.
Kungiyar NMA ta zargi Amina Abdullahi da aka fi sani da Amina HOD da cin zarafin wata likita a lokacin da ta ke tsaka da aikin kula da marasa lafiya.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng