Bayan Shiga Ofis, Sabon Ministan Tinubu Ya Fadi Ayyukan Farko da Zai Fara Aiwatarwa
- Ministan sabuwar ma'aikatar harkokin dabbobi, Alhaji Idi Mukhtar Maiha ya shaida cewa zai zamanantar da harkar kiwo
- Alhaji Idi Maiha ya ce akwai bukatar magance rikicin manoma da makiyaya ta hanyar inganta kiwo da kuma amfani da fasaha
- A yayin jawabinsa na farko ga ma'aikatan tarayyar, ministan ya ce an kafa ma'aikatar ne domin magance matsalolin fannin
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Abuja - Sabon ministan ma’aikatar dabbobi, Alhaji Idi Mukhtar Maiha da shugaba Bola Tinubu ya nada ya yi magana kan ayyukan da zai fara aiwatarwa.
Alhaji Idi Maiha, ya ce aikinsa na farko farko da zai fara aiwatarwa shi ne tabbatar da zamanantar da harkar kiwo a kasar nan.
Minista ya yi wa ma'aikata jawabin farko
Ministan ya bayyana hakan ne a jawabin farko da ya yiwa ma'aikatan sabuwar ma'aikatar ta harkokin dabbobi a Abuja, a cewar rahoton jaridar Daily Trust.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A jawabinsa, Alhaji Maiha ya ce an kafa ma’aikatar kiwon dabbobi ne domin a zamanantar da bangaren tare da magance kalubalen da fannin ke fuskanta.
A cewar ministan:
“A matsayina na mai sana’ar kiwon dabbobi, ban manta da kalubalen da wannan fanni ke fuskanta ba. Akwai tarin matsaloli amma na yi imanin cewa za a iya shawo kansu."
Kalubalen da harkar kiwo ke fuskanta
Ministan ya bayyana wasu matsaloli da harkar kiwo ke fuskanta a kasar da suka hada da tsadar abincin dabbobi da barkewar cututtuka.
Jaridar Leadership ta rahoto cewa sauran matsalolin da Alhaji Maiha ya zayyana sun hada da:
"Rikicin makiyaya da manoma, kiwo fiye da kima, tsufan dabbobi, sauyin yanayi, rashin samun bashi da wuraren kiwo da kuma rashin amfani da fasahohin zamani."
Ministan ya ce manyan ayyukan da zai fara yi sun hada da tabbatar da cewa manufofi da shirye-shiryen kasar nan sun karfafa masu ruwa da tsaki a fannin.
Ayyukan da ministan zai fara yi
Alhaji Maiha ya ce zai tabbatar tsare tsaren gwamnati sun amfani kanana da manyan masu harkar kiwo domin bunkasa fannin.
"Za mu samar da yanayin kiwo mai kyau, za mu zamanantar da harkar kiwo. Hakazalika, za mu samar da hanyar kiwo mai dorewa domin magance fadan makiyaya da manoma.
"Za mu tabbatar da cewa matasa maza da mata sun shiga harkar kiwo domin samar da ayyukan yi da kuma inganta rayuwa da yalwar arziki."
- A cewar ministan.
Tinubu ya kirkiro sabuwar ma'aikata
Tun da fari, mun ruwaito cewa shugaba Bola Tinubu ya kirkiro sabuwar ma'aikatar tarayya da ya lakabawa suna 'ma'aikatar kiwon dabbobi'.
An sanar da kirkirar ma’aikatar ne a yayin kaddamar da kwamitin aiwatar da gyara kan harkokin kiwon dabbobi a fadar shugaban kasa.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng