"Ban Sani Ba sai daga Baya," Gwamna Abba Ya Faɗi Abin da Ya Faru da Yaran Kano

"Ban Sani Ba sai daga Baya," Gwamna Abba Ya Faɗi Abin da Ya Faru da Yaran Kano

  • Gwamna Abba Kabir Yusuf ya ce bai san an kama ƙananan yara a Kano ba sai da aka gurfanar da su a gaban babbar kotun tarayya
  • Abba ya ce nan take ya ɗauki mataki kuma yamzu ga shi an sako yaran bayan shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu ya tsoma baki
  • Abba Gida Gida ya bayyana haka ne a asibitin da aka kai yaran domin samun kulawar likitoci kafin a maida su hannun iyayensu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Kano - Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, ya ce bai san an kama kananan yaran jihar ba har sai da aka gurfanar da su a gaban babbar kotun tarayya da ke Abuja.

Kara karanta wannan

Kaduna: Gwamna ya tarbi yara 39 da aka sako, ya gwangwaje su da kyaututtuka

Ya faɗi haka ne a asibiti na musamman na Muhammadu Buhari da ke Kano, inda aka ware kwararrun likitocin domin duba lafiyar yara 76 da aka sako.

Gwamna Abba Kabir Yusuf.
Gwamna Abba ya ce daga baya ya samu lamarin kama yaran Kano a lokacin zanga-zanga Hoto: Abba Kabir Yusuf
Asali: Twitter

Gwamna Abba ya godewa Bola Tinubu

Gwamnan ya mika godiya ga shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu bisa karamci da tausayi da ya nuna wa yaran, kamar yadda The Nation ta ruwaito.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Ina samun labarin yaran na tsare, ban yi wata wata ba na umarci Antoni Janar kuma kwamishinan shari'a ya gaggauta duba lamarin."
"Muna godiya ga duk wanda ke da hannu wajen tabbatar da dawowar kananan yaran lafiya, na yabawa iyayen yaran nan bisa yadda suka dage da addu'o'i tun kama yaransu har aka sako su."

- Abba Kabir Yusuf

Abba zai sa kananan yaran a makaranta

Gwamna Abba ya kara da cewa gwamnatinsa za ta ɗauki nauyin komai daga nan har lokacin da za a maida su hannun iyayensu

Kara karanta wannan

Lauyan yara da su ka yi zanga zanga ya fadi yadda gwamna Abba ya agaza masu

Ya ce zai kuma ba su tallafin da ya dace domin dukkansu idan sun koma gida su kama ƴan sana'o'in da za su iya dogaro da kansu.

Gwamnan ya kuma jaddada muhimmancin neman ilimi, ya tabbatar da cewa yaran za su koma makaranta don su samu ilimi har su ba da gudummuwa a gaba.

"Zan tabbatar da cewa waɗannan yaran sun samu wata dama ta hanyar sanya su a makaranta da kuma ba su tallafin da za su taimaki kansu," in ji Abba.

Lauya ya faɗi taimakon da Abba ya yi masu

A wani rahoton, an ji cewa Barista Hamza Nuhu Dantani ya ce gwamna Abba Kabir Yusuf ya jajirce a wajen ceto yaran Kano da aka garkame.

Lauyan ya yabi gwamnatin Kano kan yadda gwamna da kansa ya kira shi a kan matsalar yaran da aka tsare tun cikin watan Agusta.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262