An Tunkari Sarakunan Yarabawa da Buƙatar Raba Najeriya

An Tunkari Sarakunan Yarabawa da Buƙatar Raba Najeriya

  • Wata kungiyar matasa ta bukaci sarakunan Kudu maso Yammacin Najeriya da su taimakawa fafutukar kafa kasar Yarabawa
  • Kungiyar ta ce babu abin da ya fi dacewa da Yarabawa kamar ficewa daga Najeriya da kafa kasarsu domin su gina tattalin arziki
  • Yan kungiyar sun ce Allah ya albarkace su da abubuwa da dama kuma babu maganar yin kasa a gwiwa a kan ɓallewa daga Najeriya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Nigeria - Kungiyar matasan Yarabawa ta Yoruba National Youth ta yi kira ga sarakunan gargajiya kan raba Najeriya.

Kungiyar ta buƙaci dukkan sarakunan Yarabawa su fito ƙarara su nuna musu goyon baya kuma ta yi Allah wadai da masu nokewa.

Kara karanta wannan

'Mun shiga uku': Inji Mazauna yankunan da yan bindiga suka addaba kan rasuwar Lagbaja

Yarabawa
Masu fafutukar kafa kasar Yarabawa sun nemi taimakon sarakuna. Hoto: SOPA Images
Asali: Getty Images

Jaridar Vanguard ta wallafa cewa shugabannin kungiyar, Ayodele Ologunloluwa da Oyegunle Omotoyele ne suka yi kira ga sarakunan.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An turawa sarakuna buƙatar raba Najeriya

Kungiyar Yoruba National Youth ta rubuta wasika ga dukkan sarakunan gargajiya a Kudu maso Yamma domin goyon bayan raba Najeriya.

Matasan sun ce lokaci ya yi da sarkaunan za su fito ba tare da wani tsoro ba su goyi bayan ficewarsu daga Najeriya.

Yan kungiyar sun ce babu maganar cigaba da zama a Najeriya kuma babu wanda zai iya shawo kansu a kan hakan.

"Mun ki jinin duk wani kira na cigaba da zaman Yarabawa a Najeriya kuma za mu tabbatar da cewa mun kafa kasa.
Duk wani sarki da bai fito fili ya goyi bayan wannar tafiyar ba, za mu dauke shi a matsayin makiyin kasar Yarabawa."

- Kungiyar matasan Yarabawa

Kara karanta wannan

'An samu gibi': Ministan tsaro ya magantu kan rasuwar Lagbaja, ya fadi tasirinsa a tsaro

Matasan Yarbawa suna so a barka kasa

A karshe, ƙungiyar ta tabbatar da cewa wannan aikin da ta dauko za ta cigaba da shi har sai ta samar da kasar Yarabawa.

Matasan sun ce abin Allah wadai ne yadda wasu sarakuna ke cigaba da kira a kan su cigaba da zama a Najeriya.

An kama masu neman kafa kasar Yarabawa

A wani rahoton, kun ji cewa wata kotun Majistare dake zamanta a Ibadan ta bayar da umarnin tisa keyar wasu mutane 29 gidan gyaran hali.

An zargi masu fafutukar kafa kasar Yarabawan da yunkurin kai hari gidan gwamnatin jihar Oyo tare da yi wa sakatariyar gwamnati da'ira.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng