Rikicin NNPP Ya Jawo Cire Wasu Manyan Sakatarori a Kano? Gwamnati Ta Yi Magana
- Gwamnatin Kano ta yi martani kan zargin alakar siyasa da sauye-sauyen ma'aikatu da aka yi wa wasu manyan daraktoci da sakatarori
- A wata sanarwa ta musamman, Gwamnatin ta ce sam babu kamshin gaskiya kan abin da ake yadawa cewa rikicin NNPP ta jawo haka
- Wannan na zuwa ne yayin da ake zargin rigima ta barke a jam'iyyar NNPP da kuma tsakanin Abba Kabir Yusuf da Kwankwasiyya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Kano - Gwamnatin Kano ta yi magana kan zargin sauya wasu manyan sakatarori a jihar saboda zargin rikicin NNPP.
Ofishin shugaban ma'aikatan jihar Kano ta musanta alakar cire manyan sakatarorin a dalilin rikicin da ake zargin ya barke a NNPP.
Gwamnatin Kano ta magantu kan cire manyan sakatarori
Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da hadimin Gwamna Abba Kabir a bangaren sadarwa, Abdullahi Ibrahim ya wallafa a shafin X.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A cikin sanarwar shugaban ma'aikata Abdullahi Musa ya musanta labarin, ya ce babu kamshin gaskiya a ciki.
Musa ya ce an shirya labarin ne domin kawo cikas ga gwamnatin Abba Kabir saboda cimma wasu manufofi.
'Babu alakar siyasa da sauye-sauyen': Gwamnatin Kano
"Wannan sauye-sauye da aka yi na manyan sakatarori na daga cikin tsarin aiki da kuma inganta aikin gwamnati a Kano."
"Hakan ya biyo bayan shirin murabus na manyan sakatarori da daraktoci a jihar da aka shirya a watan Disambar 2024."
"Wannan sauye-sauye ya shafi ma'aikatu da hukumomi daban-daban a jihar wanda bai da alaka da siyasa ko wata matsala."
- Abdullahi Musa
Abba ya magantu kan cin amanar Kwankwasiyya
Kun ji cewa Gwamnan Kano, Abba Kabir ya nuna ɓacin ransa kan masu kiraye-kirayen tsaya da ƙafarka, ya ce wannan cin mutunci ne.
Abba ya bayyana cewa masu wannan surutun su na nufin bai ma san abin da yake yi ba duk da ɗimbin ayyukan da gwamnatinsa ke yi a Kano.
Gwamman ya yi kira ga masoyansa a kowane ɓangare na rayuwa da kar su sake ambatar Abba tsaya da kafarka a Kano ko a Najeriya baki ɗaya.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng