Majalisa Ta Fitar da Sabon Kuduri da zai Yi wa Kujerar Shugaban Kasa Barazana
- Kudurin tilastawa shugaban kasa bayyana a gaban majalisun kasar nan ya tsallake karatu na daya a majalisar wakilan Najeriya
- Wannan kuduri ya kunshi abubuwa da dama, daga ciki akwai tabbatar da shugaban kasa ya ba da bahasin jagorancin da ya yi a shekara
- Matukar wasu daga cikin yan majalisun ba su gamsu da irin ayyukan da shugaban ya ke yi ba, su na da damar kokarin fara tsige shi
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT Abuja – Majalisar wakilan kasar nan ta bijiro da kudirin da zai rika sa wa shugaban kasa linzami kan gudanar da gwamnati.
Kudurin zai tilastawa shugaban kasa ya rika bayyana a gaban majalisun kasar nan biyu a kowace karshen shekara domin bayar da bayanai.
Jaridar Nigerian Tribune ta wallafa cewa shugaban zai rika fayyace ayyukan da gwamnatinsa ta yi a shekarar gabanin gabatar masu da kasafin kudin shekara ta gaba.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Majalisar tarayya ta bijiro da sabon kuduri
Kudurin da zai yi wa shugaban kasa linzami da tabbatar da irin ayyukan da ake yi ga kasa ya tsallake karatu na daya a majalisar wakilai.
Dan majalisa kuma shugaban kwamitin harkokin fetur, Ikenga Ugochinyere na son a yi wa sashe na 67 da 81 gyaran fuska.
Hakan ya na nufin za a gyara karamin sashe na 1, a kuma kara kananan sashe na 3, 4, da 5.
Ikon da kudurin zai ba 'yan majalisa
Sabon kudurin zai ba yan majalisar da ba su gamsu da ayyukan shugaban kasa ba damar kada kuri’ar rashin amincewa da salon mulkinsa.
Sannan za su iya fara neman a tsige shugaban daga kan kujerarsa matukar ayyukan da ya yi bai gamsar da yan majalisar ba.
Tinubu: Ana shirin hada kan yan majalisa
A baya kun ji cewa ana kokarin hada kan yan majalisar kasar domin bijirewa duk wani yunkuri na gwamnatin Bola Tinubu na kara haraji.
Sanata Ali Ndume daga jihar Borno da Sani Aliyu Madakin Gini daga Kano sun sha alwashin kin goyon bayan sabon kudurin a majalisunsu.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng