An Yi Artabu da Askawaran Zamfara, 'Yan Ta'adda Sun Ji Babu Dadi

An Yi Artabu da Askawaran Zamfara, 'Yan Ta'adda Sun Ji Babu Dadi

  • Yan ta’adda sun gamu da zaratan Askarawa a jihar Zamfara inda aka fatattake su a lokacin da su ke kokarin kai hari wani kauye
  • Miyagun yan bindiga sun yi yunkurin kai hari kauyen Gidan Dawa da ke karamar hukumar Tsafe da daddare jama'a na bacci
  • Mutum guda ya ji rauni, amma Askawaran sun ba yan bindiga kashi wanda ya sanya miyagun tserewa domin tsira da rayuwarsu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Zamfara – Dakarun tsaron sa kai na jihar da aka fi sani da Askarawa sun yi artabu da yan ta’adda da su ka yi kokarin kai hari jihar Zamfara.

Kara karanta wannan

Zanga zanga: Kashim Shettima zai tarbi yara bayan gwamnati ta janye shari'a a kotu

Yan ta’addan sun yi kokarin kutsawa kauyen Gidan Dawa da ke karamar hukumar hari domin kai hari inda za su iya garkuwa da mutane ko su hallaka su.

Zamfara
Askarawa sun kori yan bindiga a Zamfara Hoto: Legit.ng
Asali: Original

A labarin da ya kebanta da jaridar Zagazola Makama, Askarawan sun yi tsayin daka a yayin artabun da su ka yi a kokarin hana kai hari kan bayin Allah.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Askarawan Zamfara sun kora yan ta’adda

Askarawan Zamfara sun yi nasarar dakile wani hari da yan bindiga su ka kitsa kai wa mutanen kauyen Gidan Dawa da ke karamar hukumar Tsafe.

Miyagun yan ta’addan sun kai harin da daddare da niyyar illata jama’a kafin a farga, amma Askawara sun ankara, kuma sun mayar da martanin gaggawa.

An samu rauni a fafatawar Askarawa da yan ta’adda

Mutum daya da ke kauyen Gidan Dawa ya samu rauni a lokacin da Askawara ke kokarin fatattakar yan ta’addan.

Kara karanta wannan

Sojojin sama sun yi ajalin 'yan ta'adda da ke kokarin hana gyara lantarkin Arewa

Amma an yi nasara, domin Askawaran sun kora yan bindiga wadanda su ka tsere tare da jingine yunkurin dura kan jama’a.

Yan ta'adda sun kai hari Zamfara

A baya mun ruwaito cewa yan bindiga sun kai mummunan hari jihar Zamfara tare da sace mutane sama da 100 da su ka hada da mata da kananan yara da kuma limamin garin Yankin Wankin.

Rahotanni sun bayyana cewa baya ga satar mutanen daga Sabon Layi da Dogon Hayi da yan ta’addan su ka yi, sun kora shanu masu tarin yawa zuwa daji ba tare da an samu mai hana su ba.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.