Dangote Ya Shiga Matsala, AYM Shafa da A.A Rano Sun Shigar da Kara a Kotu

Dangote Ya Shiga Matsala, AYM Shafa da A.A Rano Sun Shigar da Kara a Kotu

  • Wasu manyan yan kasuwa a harkar man fetur sun mayar da martani kan korafin attajirin Afrika, Alhaji Aliko Dangote
  • Kamfanonin AYM Shafa da A. A Rano da Matrix sun bukaci kotu ta dakatar da Dangote daga mamaye kasuwar mai
  • akan ya biyo bayan korafi da Dangote ya shigar kan dakatarwa da kwace lasisinsu na shigo da mai daga ketare

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - An shiga kotu da attajirin dan kasuwa, Alhaji Aliko Dangote kan mamaye bangaren makamashi.

Manyan yan kasuwa uku a Najeriya sun bukaci kotu da dakatar da Dangote daga mamaye bangaren mai a kasar.

Yan kasuwa sun maka Dangote a kotu
Manyan yan kasuwa sun bukaci kotu da dakile Aliko Dangote mamayar bangaren mai shi kadai. Hoto: Bloomberg.
Asali: Getty Images

Dangote ya bukaci dakatar da shigo da mai

Kara karanta wannan

Majalisa ta fitar da sabon kuduri da zai yi wa kujerar shugaban kasa barazana

Vanguard ta ce AYM Shafa da A. A Rano da kuma Matrix su suka bukaci kotun da dauki mataki saboda shawo kan fadawa matsala a kasar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kamfanonin sun dauki matakin ne bayan Dangote ya yi korafi a kwace lasisinsu na shigo da mai daga ketare.

Hakan ya biyo bayan zargin da Dangote ke yi musu kan shigo da mai marar inganci daga ƙasashen waje.

Yan kasuwa sun shiga kotu da Dangote

Lamarin ya sanya fargaba daga ɓangaren yan kasuwar da suke ganin Dangote na kokarin zama mai juya alakar komai a bangaren.

Yan kasuwar suka ce barin matatar Dangote mamaye bangaren zai kawo cikas ga cigaban Najeriya, Punch ta ruwaito.

Sun bukaci Babbar Kotun Tarayya ta dakile Dangote saboda zai zama shi kadai ke da iko a bangaren.

Har ila yau, suka ce bai kamata Dangote ya mayar da bangaren kaman na shi shi kadai ba, duba da yawan yan kasuwa da ake damawa da su.

Kara karanta wannan

Tinubu ya shirya gwangwaje ƙananan yan kasuwa, ya fadi ka'idojin cin gajiyar N75bn

Dangote ya nemo mafita kan wahalar mai

Kun ji cewa Shugaban rukunin kamfanonin Ɗangote Group, Aliko Ɗangote ya ce matatarsa tana da isasshen fetur da zai kawar da dogon layi.

Attajirin ɗan kasuwar ya buƙaci kamfanin mai na ƙasa watau NNPCL da ƴan kasuwa su daina shigo da mai daga ƙasashen ketare.

Alhaji Aliko Ɗangote ya bayyana haka ne a wata hira da manema labarai a fadar shugaban ƙasa bayan ganawa da Bola Ahmed Tinubu.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.