Ana Fama da Rashin Wuta, Kamfanonin Lantarki Sun Kara Kudin Mita

Ana Fama da Rashin Wuta, Kamfanonin Lantarki Sun Kara Kudin Mita

  • Kamfanonin rarraba hasken lantarki da ake kira da DisCos sun kara daga farashin mita ga abokan huldarsu a kasar nan
  • Wannan shi ne karo na biyu da kamfanonin su ka kara farashin a cikin watanni hudu, tun bayan kara kudi a watan Agusta
  • An kara akalla 28.03% na kudin da ake biya a baya, yanzu mita ta kai tsakanin N117,000 zuwa N149,800 a wasu kamfanonin

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT Abuja – Kamfanonin rarraba hasken lantarki (DisCos) sun sanar da kara kudin mitar lantarki da abokan huldarsu ke amfani da su.

Wannan na zuwa ne bayan kamfanonin sun yi karin kudin mita a kwanakin baya, wanda ke nufin an yi karin sau biyu a cikin watanni hudu.

Kara karanta wannan

Gwamnati ta soke kwangilar N740bn, aikin titin Abuja zuwa Kaduna ya tsaya cak

Lantarki
DisCos sun kara kudin wuta Hoto: Olasukanmi Ariyo
Asali: Getty Images

Jaridar Vanguard ta wallafa cewa an kara kudin mita daga N117,000 zuwa N149,800 wanda ke nuna karin akalla 28.03% ko kuma N32,800.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sabon kudin mitar lantarki ya fara aiki

Jaridar Punch ta wallafa cewa sabon karin kudin sayen mita da kamfanonin rarraba lantarki suka yi ya fara aiki a ranar 5 Nuwamba, 2024.

Wannan na nuna cewa hukumar kula da wutar lantarki ta kasa (NERC) ta tsame hannunta daga batun saye da sayar da mita ga masu bukata.

Yadda DisCos su ka kara kudin mitar lantarki

An samu banbancin farashin mitocin tsakanin kamfanonin, inda kamfanin wuta na Eko ya ke sayar da mita mai fuska daya a farashin N135,987.5 zuwa N161,035.

Kamfanin da ke Kano ya na sayar da mita mai fuska daya a kan N127,925–N129,999 mai fuska uku kuma ana sayar da ita a kan N223,793 - NN235,425.

Kara karanta wannan

Manyan abubuwa 3 da gwamnatin Tinubu ta fusata Mutanen Arewa da su

An gano dalilin matsalolin lantarki

A baya mun wallafa cewa gwamnatin Bola Ahmed Tinubu ta kafa kwamiti karkashin jagorancin Injiniya Nafisatu Asabe Ali domin bincike da gano abin da ke jawo yawaitar matsalolin lantarki.

Kwamitin ya gano wasu manyan matsaloli da su ka hada da samar da wuta mai karfin gaske da ya lalata hanyar lantarkin, rashin gyara a kai a kai, kuma kayan da ke bangaren sun tsufa.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.