'Mun Shiga Uku': Mazauna Yankunan da Yan Bindiga Suka Addaba kan Rasuwar Lagbaja

'Mun Shiga Uku': Mazauna Yankunan da Yan Bindiga Suka Addaba kan Rasuwar Lagbaja

  • Ana cigaba da alhini da tura sakon jaje ga Shugaba Bola Tinubu da sauran yan Najeriya kan rasuwar hafsan sojoji, Taoreed Lagbaja
  • Kungiyar mazauna yankin Birnin Gwari da iyakar jihar Niger sun nuna damuwa kan babban rashin da aka yi
  • Kungiyar BG-NI CUPD ta ce yan Najeriya za su yi kewarsa musamman wadanda ke fama da rashin tsaro a yankunansu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Kaduna - Mazauna yankin Kaduna da Niger sun nuna alhini kan rasuwar hafsan sojoji, Laftanar-janar Taoreed Lagbaja.

Mazauna iyakar jihohin biyu da ke fama da matsalolin yan bindiga suka ce rashin Lagbaja babban gibi ne a yaƙi da matsalar tsaro.

Kara karanta wannan

Pantami ya yi alhinin rasuwar Janar Taoreed Lagbaja, ya yi masa addu'a

Yan Najeriya sun yi alhinin rasuwar hafsan sojoji, Lagbaja
Mazauna yankin Kaduna da Niger sun yi jajen rasuwar hafsan sojoji, Laftanar-janar Taoreed Lagbaja. Hoto: HQ Nigerian Army.
Asali: Twitter

Yan Najeriya sun yi alhinin rasuwar Lagbaja

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kungiyar yankin Birnin Gwari da iyakar Niger (BG-NI CUPD) ta kadu da rasuwar marigayin duba da gudunmawarsa, cewar Premium Times.

Shugaban kungiyar, Ishaq Kasai shi ya tabbatar da haka a cikin wata sanarwa a jiya Laraba 6 ga watan Nuwambar 2024.

Kasai ya ce yan Najeriya za su yi kewar Lagbaja musamman wadanda ke fama da matsanancin rashin tsaro a yankunansu.

Kokarin Taoreed Lagbaja a yaƙi da ta'addanci

Shugaban kungiyar ya ce kungiyoyin ta'addanci kamar su Al-Qaeda da Ansaru da yan bindiga da Boko Haram sun addabi yankunan.

Sai dai ya ce zuwan marigayi Lagbaja ya dakile matsalolin da dama inda ya hallaka yan ta'adda inda ya ba sabon mukaddashin hafsan sojojin shawara.

"Shugabancinsa a gidan soja ya karawa mazauna yankunan karfin guiwa musamman yadda ake fama da miyagu."

Kara karanta wannan

'Jarumi ne': Buhari ya jajanta mutuwar Lagbaja, ya fadi farkon ganinsa a gidan soja

"Yana da muhimmanci sabon mukaddashin hafsan sojojin ya bi sahun Lagbaja domin dakile matsalolin yan bindiga da ake fama da su."
"Muna mika sakon ta'azziya ga Bola Tinubu da iyalan mamacin da sauran yan Najeriya kan wannan babban rashi."

- Ishaq Kasai

Buhari ya jajanta rasuwar hafsan sojoji, Lagbaja

Kun ji cewa tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya kadu da samun labarin rasuwar hafsan sojoji, Laftanar-janar Taoreed Lagbaja.

Buhari ya ce tabbas an yi babban rashin jarumi inda ya tuno lokacin da ya fara ganinsa a gidan soja a lokacin yana shugaban kasa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.