Zanga Zanga: Sanusi II Ya Ci Gyaran Yan Sanda, Ya Dubo Yaran da Aka Kai Kotu
- Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II ya gana da yaran da Bola Tinubu ya yi wa afuwa kan shiga zanga zangar tsadar rayuwa
- Muhammadu Sanusi II ya buƙaci jami'an tsaro su canja salon kama masu laifi idan aka samu tarzoma ko rikici a tsakanin al'umma
- Sarkin ya kuma yabawa shugaba Bola Tinubu da gwamna Abba Kabir Yusuf kan ganin yaran sun samu yanci bayan kulle su da aka yi
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Kano - Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II ya yi kira na musamman ga jami'an tsaro kan kama masu zanga zanga.
Muhammadu Sanusi II ya yi magana ne yayin da ya ziyarci yaran zanga zangar Kano da aka dawo da su daga birnin Abuja.
Jaridar Vanguard ta wallafa cewa Sanusi II ya ce yawancin yaran da aka kama ba masu zanga zangar ba ne.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Muhammadu Sanusi II ya ziyarci 'yan zanga zanga
Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II ya ziyarci yaran zanga zangar Kano a asibitin Muhammadu Buhari da ke kwaryar jihar.
The Guardian ta wallafa cewa Sanusi II ya ziyarci yaran ne domin duba lafiyarsu bayan an dawo da su daga Abuja sakamakon afuwa da aka yi musu.
A sauya salon kama mutane inji Sanusi II
Mai martaba Muhammadu Sanusi II ya bukaci a rika bincike da adalci wajen kama masu laifi na hakika idan aka samu tarzoma.
Sarkin Kano ya ce dole a rika tabbatar da cewa an kama wadanda suka yi laifi idan aka samu tarzoma ba yara ƙanana ba.
"Bisa tambayoyi da na masu, na fahimci an kama mafi yawan yaran ne yayin da suke dawowa daga makaranta ba wai a tsakiyar zanga zangar ba.
Saboda tabbatar da adalci, ya kamata a rika kama wadanda suka yi laifi a gurfanar da su ba yara da ba ruwansu ba."
- Muhammadu Sanusi II
Sarkin ya ce da an cigaba da azabtar da su, da mafi yawansu sun mutu, saboda haka ya yi godiya ga Bola Tinubu da Abba Kabir wajen kawo karshen lamarin.
An ba yaran zanga zanga kudi a Kaduna
A wani rahoton, kun ji cewa gwamnan Kaduna Uba Sani ya bai wa yaran Kaduna da aka sako kyautar N100,000 da manyan wayoyin hannu na zamani.
Mai girma Uba Sani ya kuma yi alƙawarin ci gaba da tallafa masu a wurin taron miƙa kowane yaro ga iyayensa ko ƴan uwa a Kaduna.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng