Kwamitin Tinubu Ya Bankado Matsaloli 2 da ke Jawo Yawan Lalacewar Wuta
- Kwamitin da gwamnatin tarayya ta kafa domin gano dalilin yawaitar matsalar lantarki a kasar nan ya fitar da rahotonsa
- Injiniya Nafisatu Asabe Ali ce ta ke jagorantar kwamitin da ake ganin zai fadi matsalolin da bangaren lantarki ke fuskanta
- Kwamitin ya bankado abubuwan da ke jawo ake yawan lalacewar wuta, inda daya daga cikin dalilan ya jibanci tsufan kayan lantarki
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT Abuja – Gwamnatin tarayya ta ce ta gano matsalar da ke jawo yawan lalacewar wutar lantarki a Najeriya.
Ikirarin na zuwa ne bayan tashar da ke sada yan kasa da hasken lantarki ya lalace a karo na 10 a shekarar 2024.
Jaridar Punch ta wallafa cewa gwamnatin Bola Ahmed Tinubu ta kafa kwamiti da zai yi bincike domin gano musabbabin yawaitar matsalolin lantarki don magance su.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Matsalar lantarki: Kwamitin gwamnati ya yi bayani
Jaridar Daily Trust ta tattaro cewa kwamitin gwamnatin tarayya a kan matsalolin lantarki ya dangantaka yawaitar lalacewar turakun wuta a kan tsofaffin kayan lantarki da ake da su.
Kwamitin karkashin jagorancin Injiniya Nafisatu Asabe Ali ya kuma gano cewa ba a cika gyara kayan lantarkin akai akai kamar yadda ya dace ba.
Kwamitin Tinubu ya fadi matsalar lantarki
Kwamiti da gwamnatin tarayya ta kafa domin gano matsalolin wutar lantarki ya binciko yadda aka samar da wuta mai karfi wanda ya fi karfin kayan aikin da ake da su.
Kwamitin ya bayyana cewa wannan shi ne dalilin da kasa ta shiga duhu a ranar 14 da 19 Oktoba, 2024.
A bangarensa, Ministan makamashi, Adbebayo Adelabu ya ce zai tabbatar da an karawa sashen lantarki kasafin kudi domin magance wasu daga cikin matsalolin.
Wutar lantarki ya sake lalacewa a Najeriya
A wani labarin mun ruwaito cewa kasar nan ta sake fuskantar gagarumar matsalar lantarki da ya jefa ta a cikin duhu bayan tashar wutar lantarki ta sake lalacewa a karo na 10 a ranar Talata.
Lalacewar tashar lantarki ya jawo rashin wuta da kamfanonin lantarki za su rabawa abokan huldarsu, kuma wannan na zuwa a gabar da ake kokarin dawo da hasken wuta ga Arewa.
Asali: Legit.ng