Matasa Ƴan NYSC Sun Yi Magana kan Fara Biyan Sabon Alawus na N77,000 a Wata
- Masu yiwa ƙasa hidima da aka fi sani da ƴan NYSC sun koka kan rashin aiwatar da sabon alawus da gwamnati ta yi alƙawari N77,000
- Matasan sun roki gwamnatin tarayya ta cika alkawarin da ta ɗauka saboda a halin da ake ciki N33,000 ba ta ɗaukarsu a wata
- A kwanakin baya gwamnatin tarayya karkashin Bola Tinubu ta sanar da ƙarawa matasan alawus zuwa N77,000 duk wata
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Matasa masu yi wa ƙasa hidima sun roki gwamnatin tarayya karkashin Bola Tinubu ta cika alkawarin da ta ɗauka na kara masu alawus zuwa N77,000.
Matasan wadanda ke karkashin kulawar hukumar kula da masu yiwa kasa hidima watau NYSC sun koka kan cewa duba da matsin da ake ciki N33,000 ba ta isarsu a wata.
Sun bayyana kokensu ne a shafukan sada zumunta, inda suka roƙi gwamnatin Tinubu ta cika alƙawarin N77,000, kamar yadda Daily Trust ta kawo.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Matasa sun koka kan biyan N33,000
A cewarsu duk da gwamnatin tarayya ta amince da sabon mafi ƙarancin albashi a watan Yuli, 2024, har yanzu matasan suna karɓan tsohon alawus na N33,000.
Idan baku manta ba gwamnatin tarayya ta sanar ƙara alawus na matasa ƴan bautar ƙasa daga N33,000 zuwa N77,000.
A wata sanarwa da NYSC ta fitar, ƙarin zai fara aiki ne daga watan Yuli, 2024 to amma har yanzu shiru ba a fara biyan matasan sabon alawus din ba.
Ƴan NYSC sun koka kan sabon alawus
Da suke kokawa saboda tsadar rayuwar da ake ciki, matasan sun ce alawus na N33,000 da ake ba su a yanzu ba ya kai masu ko ina a wata.
A cewarsu tsadar sufuri, kudin abinci da harkokin NYSC na yau da kullum sun sa alawus din ba ya kai wa ko ina a wata.
@NoorAjuwon ya wallafa a shafinsa na X cewa:
"Watanni uku kenan amma har yanzu gwamnatin tarayya na ganin N33,000 sun isa ɗaukar ɗawainiyar matashi a wata."
@Arbdoolbasid_Jr ya yi tambaya da cewa:
"Ta yaya za mu iya mayar da hankali kan aikinmu da N33k a wannan halin na matsin tattalin arziki?
@Eze_na_ujari ya ce:
"Ina kashe N5,000 a sufuri, N2,000 na CDS, sauran N26, daga N33,000."
NYSC ta faɗi dalilin rashin fara biyan N77,000
A wani labarin, an ji cewa hukumar yi wa ƙasa hidima ta Najeriya (NYSC) ta bayyana dalilin kasa fara biyan sabon alawus ga masu yi wa ƙasa hidima.
Shugaban hukumar NYSC, ya bayyana cewa ba a fara biyan N77,000 ba ne saboda har yanzu gwamnati ba ta saki kuɗaɗen ba.
Asali: Legit.ng