Kaduna: Gwamna Ya Tarbi Yara 39 da Aka Sako, Ya Gwangwaje Su da Kyaututtuka

Kaduna: Gwamna Ya Tarbi Yara 39 da Aka Sako, Ya Gwangwaje Su da Kyaututtuka

  • Gwamnatin jihar Kaduna ta shirya tallafawa yaran da gwamnatin Bola Tinubu ta sako kan zargin shiga zanga-zanga
  • Sanata Uba Sani ya karbi bakuncin yaran inda ya yi wa kowane daya kyautar N100,000 da kuma sabuwar babbar waya
  • Uba Sani ya kuma yi alkawarin samar musu ayyukan yi tare da ba wasu daga cikinsu jari domin tsayawa da kafafunsu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Kaduna - Gwamnatin jihar Kaduna ta karbi bakuncin yara 39 da aka sako daga Abuja kan zargin zanga-zanga.

Mai girma Gwamna Uba Sani shi ya karbi yaran inda aka yi nasarar hada su da iyayensu bayan shigowa jihar Kaduna.

Uba Sani ya gwangwaje yara 39 da aka sako da kyaututtuka
Gwamna Uba Sani ya karbi bakuncin yara 39 da aka sako a Kaduna. Hoto: Uba Sani.
Asali: Twitter

Gwamna ya gwangwaje yara 39 da aka sako

Kara karanta wannan

Lauyan yara da su ka yi zanga zanga ya fadi yadda gwamna Abba ya agaza masu

Vanguard ta tabbatar cewa kowane yaro ya samu kyautar N100,000 da sabuwar waya samfurin Android' daga gwamnatin jihar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sakataren gwamnatin jihar, Dr. Abdulkadir Muazu Meyere shi ya wakilci gwamnan Uba Sani yayin karbar yaran a Kaduna.

Gwamnan ya ce a shirye yake domin tallafawa yaran saboda su zama mutanen kirki a cikin al'umma.

Kaduna: Uba Sani ya umarci karbar takardunsu

Dr. Meyere ya ce Uba Sani ya umarce su da su karbi takardun wadanda suka kammala karatun gaba da sakandare, Punch ta ruwaito.

"Gwamnan ya ce zai ba wasu a ciki jari tare da koyawa wasu sana'o'i yayin da za a ba wasunsu aikin yi."

- Dr. Abdulkadir Muazu Meyere

Za a rika bibiyar yaran da aka sako

Gwamnatin jihar za ta rika bibiyar yadda yaran ke rayuwa domin sanin ko sun sauya inda za su cigaba da cin gajiyar shirye-shirye.

Kara karanta wannan

Gwamna Abba ya aika sako ga Tinubu bayan ya karbi yaran da aka tsare

An karbi lambobin wayoyinsu da kuma adireshi domin samun sauki wurin bibiyar lamuransu bayan sun shaki iskar yanci.

Abba Kabir ya tarbi yara, ya ja kunnensu

Kun ji cewa Gwamna Abba Kabir Yusuf ya gargadi yaran da ta karbo daga hannun gwamnatin tarayya da kar su kara shiga zanga zanga.

Gwamnatin Kano ta ce babu abin da ya dace yaran su rika yi a yanzu kamar zuwa makaranta da kuma zama yan kasa na gari.

A jiya Talata yaran Kano akalla 73 su ka sauka a jihar bayan shafe tsawon lokaci a hannun jami'an tsaron kasar nan.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.