Malamin Addini Ya Hango Annoba, Ya Fadi Yadda Za a Tsira

Malamin Addini Ya Hango Annoba, Ya Fadi Yadda Za a Tsira

  • Babban fasto a kasar nan, Rabaran Ejike Mbaka ya yi gargadin yiwuwar barkewar yunwa nan gaba kadan a Najeriya
  • Ya ce akwai damuwa matuka bisa yadda yunwa ke kokarin mamaye ko ina tare da hauhawar farashi saboda tsadar fetur
  • Rabaran Mbaka wanda ke jagorantar wani baban coci a Enugu ya ba yan kasar nan mafita daga annobar kafin ta zo

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Jihar Enugu - Shugaban cocin 'Adoration,' Rabaran Ejike Mbaka, ya bayyana damuwarsa kan hauhawar farashin man fetur a kasar nan.

Rabaran Ejike Mbaka ya ce wannan babban kalubale ne da ya ke shirin jawo wata gagarumar matsala ga yan Najeriya.

Mbaka
Babban fasto ya ba da dabarar kaucewa fari Hoto: Ejike Mbaka
Asali: Facebook

Jaridar Vanguard ta wallafa cewa babban shugaban cocin ya ce amma akwai hanya da za a bi wajen kaucewa matsalar da ta ke shirin kunno kai.

Ya ce idan ba a farga da wuri ba, akwai babbar barazanar barkewar fari saboda tsananin yunwa da za a fuskanta.

Kara karanta wannan

Tinubu ya shirya gwangwaje ƙananan yan kasuwa, ya fadi ka'idojin cin gajiyar N75bn

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Rabaran Mbaka ya hango matsala

Jaridar Daily Post ta wallafa cewa Rabaran Fr Ejike Mbaka ya nuna damuwa saboda matsalar yunwa da hauhawar farashi a fadin Najeriya.

Rabaran Fr Mbaka ya dora alhakin hauhawar farashin a kan tashin gwauron zabo da farashin man fetur ya yi tun bayan da Bola Tinubu ya hau mulki.

Mbaka ya ba da shawara kan yunwa

Jagoran cocin 'Adoration' da ke Enugu, Rabaran Fr Ejike Mbaka ya shawarci yan kasar nan da su gaggauta rungumar addu'o'i domin kaucewa fari.

Ya ce matukar ba a tashi haikan ba, akwai barazanar yunwa da ake ji za ta koma fari biyo bayan yadda ake jin jiki.

Rabaran Fr Mbaka ya kuma shawarci jama'a da su rika sanya kudinsu a kasuwanci a maimakon boye su a cikin akawun saboda faduwar daraja da Naira ke fuskanta.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Tinubu ta yi magana kan yiwuwar dawo da tallafin man fetur a Najeriya

Rabaran Mbaka ya yi hasashe kan Tinubu

A baya mun ruwaito cewa shugaban cocin AMEN, Rabaran Fr Ejike Mbaka ya shawarci shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu bisa wani abu da ka iya faruwa da kasa.

Rabaran Fr Mbaka ya yi wa Tinubu barazana da cewa matukar bai bi a hankali tare da daukar shawarwarinsa ba, abinda ya afku a Nijar zai iya faruwa a tarayyar Najeriya.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.