Atiku Ya Yi Murna da Cin Zaben Trump, Ya Nemi Taimakonsa a Zaben 2027
- Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya mika sakon taya murna ga zababben shugaban Amurka
- Donald J Trump ya doke Kamala Haris bayan Amurkawa sun zabe shi ya jagorance su na tsawon shekaru takwas
- Atiku Abubakar ya bayyana fata zababben shugaban Amurka zai kara sa ido a kan tabbatar da ingantaccen zabe a Najeriya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT Abuja - Tsohon dan takarar shugaban kasa, Atiku Abubakar ya taya Donald J Trump murnar nasara a zaben Amurka.
Sakon taya murnar na zuwa bayan an tabbatar da nasarar Trump a matsayin shugaban kasar Amurka a ranar Laraba.
Jaridar The Cable ta wallafa cewa Donald Trump wanda ya yi wa jam'iyyar Republican takara ya yi nasara a zaben bayan ya lallasa Kamala Haris inda ya zama zababben shugaban Amurka na 47.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Atiku ya taya Trump murnar nasara
Atiku Abubakar ya wallafa a shafinsa na X cewa nasarar Donald Trump alama ce ta cewa mai hakuri ya na tare da riba, kamar yadda zababben shugaban ya yi nasara.
Tsohon dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar PDP ya kara da cewa jajircewar Trump zai zama abin koyi ga sauran yan siyasa a fadin duniya.
Atiku ya tura sako ga Trump
Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya bukaci zababben shugaban Amurka da ya sa ido a kan zaben kasar nan da ke tafe.
Ya bayyana fatan Donald J Trump zai ci gaba da tabbatar da ingantacciyar dimokuradiyya a Najeriya.
A sakon Atiku, ya yi fatan ba a Najeriya kadai gwamnatin da Trump zai jagoranta za ta sa ido ta fannin ingantaccen zabe ba, har da sauran sassan duniya.
Tinubu ya taya Trump murnar nasarar zabe
A baya kun ji cewa shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu ya taya zababben shugaban Amurka, Donald J Trump murnar nasarar a zaben kasar a ranar Laraba.
A wata sanarwa da hadimin shugaban kasa, Bayo Onanuga ya fitar,ya bukaci Donald Trump ta kara kulla kyakkyawar alaka tsakanin Amurka da Najeriya.
Asali: Legit.ng