Lagbaja: Gwamnoni 19 a Arewa Sun Yi Ta'aziyya, Sun Aika Sako Ga Bola Tinubu
- Gwamnonin jihohin Arewa 19 sun yi wa shugaba Bola Tinubu ta'aziyyar rasuwar hafsan sojojin ƙasa, Laftanar Janar Taoreed Lagbaja
- Shugaban kungiyar gwamnonin Arewa NSGF kuma gwamnan Gombe, Inuwa Yahaya ne ya mika sakon ta'aziyyar a wata sanarwa
- Ya ce marigayi Lagbaja mutumin kirki ne kuma soja wanda ya sadaukar da kansa domin kare martabar Najeriya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja - Yayin da Najeriya ke ci gaba da jimamin rasuwar babban hafsan sojojin ƙasa, Taoreed Lagbaja, gwamnonin jihohin Arewa sun yi ta'aziyya.
Gwamnonin jihohi 19 na Arewacin Najeriya karkashin kungiyarsu watau NSGF, sun aika sakon ta'aziyyar rasuwar Lagbaja ga shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu.
Kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito, gwamnonin sun yi wa Bola Tinubu da rundunar sojojin Najeriya ta'aziyyar wannan rashi.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Hakan na kunshe ne a wata sanarwa da shugaban kungiyar gwamnonin Arewa kuma gwamnan Gombe, Inuwa Yahaya ya fitar ta hannun kakakinsa, Ismaila Uba Misilli,
Lagbaja: Gwamnonin Arewa sun yi ta'aziyya
Gwamna Inuwa ya mika sakon ta’aziyyar ƙungiyar ga Shugaba Tinubu kan rasuwar Laftanar Janar Lagbaja, wanda ya rasu ranar Talata bayan ya sha fama da jinya.
Inuwa Yahaya ya bayyana marigayi COAS a matsayin gwarzon jami’in soji da ya yi wa kasa hidima cikin jajircewa da kwazo.
"Lagbaja ya karar da rayuwarsa yana sadaukar da kai da tabbatar da martabar Najeriya duk kuwa da ƙalubalen da ake fama na ƴan tada kayar baya, ƴan bindiga da sauransu."
Gwamnonin sun aika saƙo ga iyalin Lagbaja
Inuwa ya kuma mika sakon ta’aziyya ga matar marigayin, Mariya Lagbaja, ‘yar asalin Gombe daga Tula a karamar hukumar Kaltungo, da dukan dangisa.
Haka nan Gwamna Inuwa ya yi ta'aziyya ga gwamnati da al'ummar Osun, jihar da marigayin ya fito.
Shugaban gwamnonin Arewa ya yi addu'ar Allah ya jiƙan mamacin ya kuma bai wa ƴan uwansa haƙuri da juriyar wannan rashi, Punch ta kawo a rahotonta.
Bola Tinubu ya ɗage taron FEC
A wani rahoton, an ji cewa Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya ba da umarnin dage taron majalisar zartarwa bayan rasuwar Laftanar Janar Taoreed Lagbaja
Legit Hausa ta rahoto cewa hafsan sojojin kasan, Lagbaja ya rasu ne a daren ranar Talata bayan ya yi fama da rashin lafiya.
Asali: Legit.ng