'An Samu Gibi': Ministan Tsaro Ya Magantu kan Rasuwar Lagbaja, Ya Fadi Tasirinsa a Tsaro
- Ministocin tsaro a Najeriya, Badaru Abubakar da Bello Matawalle sun yi alhinin mutuwar hafsan sojojin Najeriya
- Badaru da Matawalle sun jajantawa shugaban ƙasa, Bola Tinubu kan mutuwar Laftanar-janar Taoreed Lagbaja a jihar Lagos
- Sun nuna damuwa kan rashin da kasa ta yi inda suka ce tabbas mutuwar Lagbaja ba karamar asara ba ce ga Najeriya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
FCT, Abuja - Ministan tsaro a Najeriya, Badaru Abubakar ya yi magana kan rasuwar Laftanar-janar Taoreed Lagbaja.
Badaru ya jajantawa Shugaba Bola Tinubu kan rashin hafsan sojoji da aka yi a Najeriya inda ya ce babban rashi ne.
Badaru, Matawalle sun magantu kan mutuwar Lagbaja
Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da Badaru da kuma Bello Matawalle suka fitar a yau Laraba 6 ga watan Nuwambar 2024, cewar Voice of Nigeria.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Badaru da Matawalle suka ce mutuwar Lagbaja babban rashi ne ga Najeriya wanda cike gurbinsa zai yi wahala.
Sun yabawa marigayin, suka ce ya jajirce sosai wurin yin aiki tukuru da kuma ba da gudunmawa sosai ga kasa.
Badaru ya ba iyalan marigayin hakurin rashi
"Tabbas babu dadi, babban rashi ne ga al'umma, muna jajantawa shugaban kasa, Bola Tinubu da iyalan marigayin da yan uwansa."
"Jajirtacce ne kuma ya yi yaki a matakai da dama inda ya ba da gudunmawa mai tsoka a harkar tsaron Najeriya, tabbas mun yi babban rashi."
- Badaru Abubakar
Bello Matawalle ya ce yana da alaƙa mai kyau da Lagbaja inda ya ce ya ji dadin aiki tare da shi a lokacin da yake raye.
Badaru daga bisani ya yi addu'ar Ubangiji ya jikansa ya kuma gafarta masa tare da ba iyalansa hakurin jure rashinsa, Daily Post ta ruwaito.
Hafsan sojoji, Janar Lagbaja ya rasu
Kun ji cewa hafsan sojojin Najeriya, Laftanar-janar Taoreed Lagbaja ya rasu a daren jiya Talata 5 ga watan Nuwambar 2024 a birnin Lagos.
Fadar shugaban kasa ta fitar da sanarwa ta musamman kan mutuwar Lagbaja inda ta jajantawa iyalan marigayin da yan Najeriya.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng