'Yan Bindiga Sun Kashe Manoma 10, Sun Yi Garkuwa da Indiyawa a Arewacin Najeriya
- Wasu gungun 'yan bindiga sun kai mummunan hari karamar hukumar Rafi da ke jihar Neja inda suka kashe manoma 10
- Mazauna yankin sun bayyana cewa 'yan ta'addan sun fille kawunan manoma kuma sun tafi da kawunan a yayin harin
- Hakazalika, an samu rahoton cewa 'yan bindiga sun yi garkuwa da wasu Indiyawa gonar shinkafa a yankin Borgu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Neja - Rahotanni sun bayyana cewa wasu gungun 'yan bindiga sun kashe manoma 10 da suka hada da mata a jihar Neja.
An ce 'yan bindigar sun kashe manoman da suka fito daga garuruwan Wayam da Belu-Belu da ke karamar hukumar Rafi a jihar.
'Yan bindiga sun kashe manoma 10
Mazauna yankin sun ce an fille kawunan mutane shida daga cikin wadanda harin ya rutsa da su, kuma suka tafi da kawunan, inji rahoton Daily Trust.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sun ce mutane da dama kuma sun samu raunukan harbin bindiga inda ake kula da su a wani asibiti da ke Kagara, hedikwatar karamar hukumar Rafi.
Bala Tukur, mazaunin yankin ya shaida cewa:
“A kauyen Wayam da ke kusa da Madaka da ke karkashin garin Kagara, sun kashe mutane 10, tare da jikkata da dama. Yadda suke kashe mu yanzu ya munana."
'Yan bindiga sun sace Indiyawa a Neja
Bala Tukur, ya shaida cewa mazauna Wayam, Belu-Belu, Madaka da sauran garuruwan da ke makwabtaka da su, duk sun gudu zuwa garin Kagara tun da safiyar Talata.
Hakazalika, Aminiya ta tattaro cewa an yi garkuwa da wasu ‘yan kasar Indiya biyu a gonar shinkafa a Swashi, karamar hukumar Borgu a ranar 2 ga Nuwamba, 2024.
Wani mazaunin garin da ya so a sakaya sunansa ya ce an kashe daya daga cikin ‘yan banga da ke gadin gonar a yayin harin.
Kwamishinan tsaron cikin gida, Birgediya Janar Bello Abdullahi Mohammed ya ce gwamnatin jihar na sane da hare-haren 'yan bindigar.
'Yan bindiga sun kai hari a Kontagora
A wani labarin, mun ruwaito cewa akalla fasinjoji 22 ne 'yan bindiga suka yi awon gaba da su a yankin karamar hukumar Kontagora da ke jihar Neja.
Kakakin majalisar dokokin jihar Neja, Abdulmalik Sarkin Daji ya ce 'yan bindigar sun tafi da fasinjojin da ke tafiya a cikin motoci biyar, zuwa cikin daji.
Asali: Legit.ng