Etsako: Karamar Hukumar da Yan Bindiga ke Kashe Mutane kamar Dabbobi

Etsako: Karamar Hukumar da Yan Bindiga ke Kashe Mutane kamar Dabbobi

  • Shugabar karamar hukumar Etsako ta Gabas, Benedicta Attoh ta koka kan yadda yan bindiga da sauran miyagu ke kashe mutane
  • Hon. Benedicta Attoh ta bayyana cewa mutanen garin sun gaji da yadda kullum ake kashe su kamar ɗan Adam ba shi da daraja
  • Sarkin gargajiya a karamar hukumar ya yi kira ga gwamnatin tarayya domin ɗaukar matakin da zai kawo karshe kashe kashe

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Edo - Mutanen karamar hukumar Etsako ta Gabas a jihar Edo sun shiga takaici kan yadda aka yawaita kashe mutane a garin.

Shugabar karamar hukumar, Benedicta Attoh ta ce kusan kullum sai an kashe mutane wanda hakan ke jefa al'umma a fargaba.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun kashe manoma 10, sun yi garkuwa da Indiyawa a Arewacin Najeriya

Obaseki
Yan bindiga sun fitini karamar hukumar Etsako a Edo. Hoto: Godwin Obaseki
Asali: Facebook

Jaridar Vanguard ta wallafa cewa mutane garin sun yi kira ga gwamnatin tarayya ta kawo musu dauki a kan halin da suke ciki.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda ake kashe mutane a Etsako

Shugabar karamar hukumar Etsako ta Gabas a jihar Edo ta ce yan bindiga da makiyaya na kashe mutanen garin a kai a kai.

Benedicta Attoh ta ce kullum sai sun samu labarin an kashe mutane biyar ko abin da ya yi kama da haka.

Shugabar ta kara da cewa kisan ya jawo manoma sun fara daina zuwa gona domin neman tsira da rayuwarsu.

"Ana kashe mutane kamar dabbobi. Kullum sai mun ji labarin an kashe mutane biyar ko hudu.
Har yanzu ba mu kididdige adadin wandada aka kashe ba saboda gawar wasu mutanen na jeji.
Muna tsoron abin da zai biyo baya idan matasa suka fara daukar doka a hannu wajen daukar fansa."

Kara karanta wannan

Kwana ya ƙare: Mutane sama da 15 sun mutu a gadar sama, bayanai sun fito

- Benedicta Attoh

Sarki a garin, Peter Osigbemeh ya bukaci gwamnatin tarayya ta yi amfani da yan banga domin gadin jejin da miyagun ke buya.

Mai martaba, Peter Osigbemeh ya ce hakan na cikin hanyoyin da za a bi wajen magance matsalar tsaro a Etsako ta Gabas.

Kungiyar yan ta'adda ta ɓulla a Sokoto

A wani rahoton, kun ji cewa an samu bullar wata sabuwar kungiyar yan ta'adda daga ƙasashen waje a yankunan jihar Sokoto.

An tabbatar da cewa kungiyar Lakurawa ta fara yaudarar matasan jihar Sokoto da ba su miliyoyin kudi domin taimaka mata wajen yin ta'addanci.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng