'A Sauke Tutoci': Tinubu Ya Dauki Matakai 2 bayan Mutuwar Hafsan Sojojin Kasa

'A Sauke Tutoci': Tinubu Ya Dauki Matakai 2 bayan Mutuwar Hafsan Sojojin Kasa

  • Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya ba da umarnin dage taron majalisar zartarwa bayan rasuwar Laftanar Janar Taoreed Lagbaja
  • Legit Hausa ta rahoto cewa hafsan sojojin kasan, Lagbaja ya rasu ne a daren ranar Talata bayan ya yi fama da rashin lafiya
  • A sanarwar da Bayo Onanuga ya fitar ranar Laraba, Tinubu ya ba da umarnin sauke tutoci a fadin kasar domin girmama Lagbaja

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Abuja - Shugaba Bola Ahmed Tinubu, babban kwamandan sojojin kasar nan, ya bayar da umarnin dage taron majalisar zartaswa ta tarayya.

Shugaban kasar ya dage taron majalisar zartarwar ne sakamakon rasuwar babban hafsan sojojin kasan Najeriya, Taoreed Lagbaja.

Kara karanta wannan

'Jarumi ne': Buhari ya jajanta mutuwar Lagbaja, ya fadi farkon ganinsa a gidan soja

Tinubu ya yi magana bayan rasuwar hafsan sojojin kasan Najeriya, Lagbaja
Tinubu ya dage taron majalisar zartarwar ta tarayya saboda mutuwar hafsan sojin kasa. Hoto: @stanleynkwocha_, @HQNigerianArmy
Asali: Twitter

Tinubu ya dage taron majalisar zartarwa

Mai magana da yawun shugaban kasar, Bayo Onanuga ne ya fitar da sanarwar umarnin da Tinubu ya bayar a shafinsa na X a ranar Laraba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sanarwar Bayo Onanuga ta ce:

"Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu, babban kwamandan sojojin kasar nan, ya ba da umarnin dage taron majalisar zartarwa ta tarayya har zuwa nan gaba.
"An dage taron majalisar wanda aka shirya yi yau domin girmama Laftanar Janar Taoreed Lagbaja, babban hafsan sojin kasa, wanda ya rasu a daren ranar Talata."

Tinubu ya ba da umarnin sauke tuta

Sanarwar ta bayyana cewa Janar Lagbaja ya rike mukamin babban hafsan sojin daga ranar 19 ga watan Yuni, 2023, har zuwa rasuwarsa a ranar 5 ga Nuwamba, 2024.

Shugaba Tinubu ya kuma ba da umarnin sauke tutoci a fadin kasar na tsawon kwanaki bakwai domin karrama Lagbaja da ya rasu, a cewar Onanuga.

Kara karanta wannan

'An samu gibi': Ministan tsaro ya magantu kan rasuwar Lagbaja, ya fadi tasirinsa a tsaro

"Shugaban ya yi wa Laftanar Janar Lagbaja addu'ar samun salamana a kwanciyar kabarinsa tare da karrama gagarumar gudunmawar da ya bayar ga al’umma."

- A cewar sanarwar.

Hafsan sojojin kasa, Lagbaja ya rasu

Tun da fari, mun ruwaito cewa fadar shugaban kasa ta sanar da rasuwar babban hafsan sojojin kasan Najeriya, Taoreed Lagbaja yana da shekaru 56.

Sanarwar da fadar shugaban kasar ta fitar ta ce Laftanal Janar Lagbaja ya rasu a daren ranar Laraba bayan ya yi fama da rashin lafiya ta kwanaki.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.