Zanga Zanga: Magoya Bayan APC Sun Fantsama Majalisa kan Tsadar Rayuwa

Zanga Zanga: Magoya Bayan APC Sun Fantsama Majalisa kan Tsadar Rayuwa

  • Wasu mazauna kasar nan sun gudanar da zanga zanga a babban birnin tarayya Abuja saboda tsadar rayuwa da ake ciki a yau
  • Matasan da su ka samu jagorancin Kabir Matazu da Danielsi Momoh sun dora alhakin wahalar da ake ciki kan sha'anin fetur
  • Sun shaidawa majalisa abin da su ke bukata da a ganinsu zai kawo saukin matsalolin tsadar farashi da ake fuskanta a fadin kasar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT, AbujaYan kasar nan sun bayyana takaicin yadda wahala ta ki karewa, saboda haka su ka garzaya majalisar tarayyar Najeriya su na neman daukin mahukunta domin warware matsalar.

Kara karanta wannan

Zanga zanga: Kashim Shettima zai tarbi yara bayan gwamnati ta janye shari'a a kotu

Magoya bayan jam’iyyar APC da ke mulki karkashin inuwar APC Solidarity and Development Forum ce ta gudanar da zanga zanga a ranar Talata.

Protest
Masu zanga zanga sun dira Abuja : HurPhoto
Asali: Facebook

Jaridar Vanguard ta wallafa cewa masu zanga-zaga sun mika bukatunsu ga majalisa da su ke ganin a tunaninsu, zai kawo saukin rayuwa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yan Najeriya sun yi zanga zanga a majalisa

Jaridar Daily Nigerian ta wallafa cewa yan kasar nan da wahalar rayuwa ta ishe su sun nemi a yi garanbawul ga wasu bangarori.

Masu zanga zanga sun bayyana bukatar gwamnatin tarayya ta sake waiwayar sashen man fetur da ake zargi da jawo duk wahalar da ake ciki.

Masu zanga zanga sun mika bukata ga majalisa

Jagororin masu zanga zanga a Abuja, Kabir Matazu da Danielsi Momoh sun dora alhakin wahalar da ake sha a kasar nan a kan gazawar bangaren fetur.

Kara karanta wannan

Sojojin sama sun yi ajalin 'yan ta'adda da ke kokarin hana gyara lantarkin Arewa

A wasikar da su ka aikawa shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio kakakin majalisar wakilai, Rt. Hon. Tajudeen Abbas sun nemi a gaggauta shawo kan matsalar.

Gwamna ya tattauna da 'yan zanga zanga

A baya kun ji cewa gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf ya bukaci yaran da su zama yan kasa na gari bayan sun shaki iskar yanci bayan shafe lokaci a tsare a hannun hukumomin Najeriya.

Gwamnatin Kano ta dawo da yaran akalla 73 gida, kuma yanzu haka ana dauba lafiyarsu, inda aka hore su da kar su kara shiga wata zanga zanga da za a iya gudanarwa a nan gaba.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labari.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.