Kamfanin NNPCL Ya Yi Martani kan Zargin Shigo da Gurbataccen Fetur daga Waje

Kamfanin NNPCL Ya Yi Martani kan Zargin Shigo da Gurbataccen Fetur daga Waje

  • Kamfanin man fetur na Najeriya (NNPCL) ya taɓo batun zargin da ake yi masa kan shigo da gurɓataccen fetur cikin ƙasar nan
  • Babban jami'in sadarwa na kamfanin NNPCL ya musanta zargin, inda ya ce ko kaɗan babu ƙamshin gaskiya a cikinsa
  • Olufemi Soneye ya kuma buƙaci duk mai wata hujja kan cewa kamfanin na shigo da gurɓataccen fetur, ya fito ya bayyana ta

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Kamfanin man fetur na Najeriya (NNPCL) ya yi magana kan zargin shigo da gurɓataccen fetur cikin ƙasar nan.

Kamfanin NNPCL ya bayyana cewa ba ya shigo da man fetur mara inganci zuwa cikin ƙasar nan daga ƙasashen waje.

Kara karanta wannan

Karancin abinci: Abubuwan da suka jefa mutane cikin yunwa da mafitarsu a Najeriya

NNPCL ya musanta shigo da gurbataccen fetur
Kamfanin NNPCL ya kare kansa daga zargin shigo da gurbataccen fetur Hoto: Bloomberg
Asali: Getty Images

Babban jami'in sadarwa na kamfanin NNPCL, Olufemi Soneye, ya bayyana hakan cikin wata sanarwa a ranar Talata, cewar rahoton jaridar Vanguard.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Soneye ya bayyana haken ne yayin da yake mayar da martani ga masu zanga-zangar neman a tsige Mele Kyari, daga muƙamin shugabancin kamfanin NNPCL.

Wasu ƙungiyoyin farar hula sun gudanar da zanga-zanga a hedkwatar NNPCL da ke Abuja, domin nuna adawa da ƙarin farashin man fetur.

Me NNPCL ya ce kan shigo da gurɓataccen fetur?

Soneye ya ƙalubalanci duk mai hujjar cewa NNPCL na shigo da gurɓataccen fetur, ya fito ya kawo ta.

"Kamfanin NNPCL ba ya shigo da gurɓataccen fetur. Idan akwai waɗanda suke da shaida saɓanin hakan, su fito su kawo samfurin gurɓataccen fetur ɗin da kamfanin NNPCL ya shigo da shi."

- Olufemi Soneye

Kamfanin NNPCL ya kare Mele Kyari

Haka kuma, Soneye ya bayyana cewa Mele Kyari ba shi da alhaki kan ƙarin farashin man fetur.

Kara karanta wannan

"Cin mutunci ce": Jagora a PDP ya soki tsare yara saboda zanga zanga

Soneye ya bayyana cewa waɗanda ba su san yadda abubuwa suke ba ne kawai za su ɗora alhakin ƙarin farashin man fetur a kan Mele Kyari, rahoton da jaridar The Cable ya tabbatar.

"Idan da sun san yadda abubuwa suke, da sun gane cewa shugaban kamfanin NNPCL ba shi da alhaki kan ƙarin farashin man fetur.
"Hasalima shi ne ya tabbatar da cewa ƴan Najeriya sun samu fetur a N620 kan kowace lita fiye da shekara ɗaya, ko a lokacin da kuɗin shigo da shi ya haura N1,100."

- Olufemi Soneye

Gwamnoni sun gayyaci shugaban NNPCL

A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnonin jihohin Najeriya 36 sun yi tir da yadda matsalar fetur ta ƙi ci ta ƙi cinyewa duk da albarkar mai da ke danƙare a ƙasar.

Gwamnonin sun gayyaci shugaban kamfanin mai na Najeriya (NNPCL), Mele Kyari domin samun bayanai kan halin da sashen fetur na ƙasar nan ke ciki.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labari.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng