Ndume: Yadda za a Haɗa Kan Yan Majalisa domin Yaƙar Shirin Tinubu
- Sanata Ali Ndume ya bayyana cewa ba zai goyi bayan bukatar shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ta sauya fasalin haraji ba
- A daya bangaren, Hon. Aliyu Madaki Gini ya ce sauya fasalin haraji zai kara taimakawa wajen ruguza tattalin Najeriya
- 'Yan majalisar sun bayyana cewa za su tattaro abokan aikinsu domin yaki da bukatar shugaban kasa ta kudirin harajin
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - Bukatar shugaba Bola Ahmed Tinubu ta sauya fasalin haraji na cigaba da samun koma baya.
Sanata Ali Ndume da Hon. Ali Madaki Gini sun fito ƙarara sun nuna adawa da buƙatar Tinubu inda suka ce za su yake ta.
Channels Television ta wallafa bidiyon hirar Sanata Ali Ndume inda ya ce ana kawo buƙatar majalisa za su yi watsi da ita.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ba a bukatar ƙarin haraji inji Ndume
Sanata Ali Ndume ya bayyana cewa a yanzu haka yan Najeriya ba su bukatar a kara musu haraji saboda masifar tsadar rayuwa.
Ali Ndume ya ce a halin yanzu mutane na fafutukar neman abin da za su ci ne kuma ya kamata gwamnatin Tinubu ta tausaya musu.
Ndume: 'Za a yi watsi da bukatar Tinubu'
Sanata Ali Ndume ya ce da zarar an kawo bukatar Bola Tinubu a kan haraji a majalisar dattawa za a yi watsi da ita ba tare da karantawa ba.
Ndume ya ce ya kamata shugaban kasar ya saurari maganar gwamnonin Arewa da kwamitin tattalin arziki wajen janye buƙatar.
Yadda za a yaki Tinubu a majalisa
Daily Trust ta wallafa cewa Sanata Ali Ndume da Hon. Ali Madaki Gini sun fara shirin yaki da bukatar shugaban kasa a majalisu.
Ndume da Ali Madaki sun bayyana cewa za su tara Sanatoci da yan majalisar wakilai domin yaki da bukatar sauya fasalin harajin Najeriya.
Sun bayyana cewa yan Najeriya a yanzu ba su bukatar jin wata kalma da ta ke da alaka da haraji saboda yanayin rayuwa.
Dokar haraji ba makawa inji Tinubu
A wani rahoton, kun ji cewa fadar shugaban kasa ta yi martani kan kokarin gwamnonin Arewa na kawo cikas ga sabuwar dokar haraji ta Bola Tinubu. ke son kawowa
Gwamnatin tarayya ta ce mai girma Tinubu ba shi da niyyar cutar wani yanki na Najeriya a tsarin haraji da ya yi niyyar samarwa.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labari
Asali: Legit.ng