'Za a Sake Shiga Duhu': Gwamnati Ta Dauki Matakan Kawo Karshen Lalacewar Wuta
- Ministan makamashi ya umarci a gaggauta sauya tsofaffin na'u'rori domin dakile ci gaba da durkushewar tashar wutar lantarki
- Kwamitin da aka kafa domin magance matsalar ya gabatar da shawarwari, kuma ministan ya ba da umarnin fara aiwatar da su
- Kafin wannan umarnin, kamfanin TCN ya bayyana cewa matsalolin durkushewar tashar wutar lantarki na iya ci gaba da faruwa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Abuja - Ministan wutar lantarki, Adebayo Adelabu, ya ba da umarnin a gaggauta sauya tsofaffin na'u'rori a tashar wutar lantarki ta kasa.
Sanya sababbin kayan aiki na daga cikin wani mataki na shawarwarin da aka bayar domin dakile ci gaba da durkushewar tashar wutar lantarki ta kasar.
Akwai yiwuwar wuta za ta sake lalacewa
Mista Adebayo Adelabu ya tabbatar da cewa za a kammala maye gurbin tsofaffin kayan cikin watanni shida, kamar yadda rahoton Punch ya nuna.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ministan ya kuma umarci kamfanin TCN da sauran hukumomin da abin ya shafa da su fara aiwatar da shawarwarin kwamitin da aka kafa domin magance lalacewar wutar.
The Guardian ta ce umarnin ministan ya biyo bayan rahoton da TCN ya fitar na cewa tashar wutar ta samu matsala a safiyar ranar Alhamis, 7 ga Nuwamba.
TCN ya nuna cewa durkushewar tashar da aka sake fuskanta a karo biyu cikin sa'o'i 72 ba zai zamo na karshe ba, domin irin wannan matsalar na iya ci gaba da faruwa.
'A aiwatar da shawarwarin kwamiti' - Minista
Mai ba ministan shawara na musamman kan watsa labarai, Bolaji Tunji, a wata sanarwa, ya nakalto ministan yana cewa za a fara aiwatar da shawarwarin nan take.
Ministan ya umarci dukkanin hukumomin da abin ya shafa da su fara aiwatar da shawarwarin kwamitin wanda aka gabatar a ranar Laraba, 6 ga Nuwamba.
"Shawarwarin kwamitin suna da ma’ana sosai, kuma za su kawo mafita mai dorewa ga matsalolin durkushewar tashar wutar da aka dade ana fuskanta a kasar nan."
- Adebayor Adelabu
'Yan Najeriya sun fusata da lalacewar wuta
A wani labarin, mun ruwaito cewa 'yan Najeriya sun nuna bacin ransu sosai game da sake durkushewar tashar wutar lantarki karo na biyu a cikin kwanaki uku.
Yayin da wasu ke neman a sanya tashar wutar a cikin addu'a, Nura Haruna ya nemi shugaba Bola Tinubu ya dauki matakan gaggawa na kawo karshen lalacewar wutar.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng