Dangote na Fuskantar Kalubale, Jiragen Ruwa Makare da Man Fetur Sun Iso Najeriya
- Hukumar kula da tashoshin jiragen ruwa ta Najeriya ta ce jiragen ruwa dauke da lita militan 101.9 sun iso tashoshin ruwan Legas
- A cikin rahoton NPA da aka gani, an gano cewa jiragen ruwa 10 dauke da kayayyaki daban daban sun iso Najeriya a makon nan
- Wannan dai na zuwa ne yayin da matatar man Dangote ta fara aiki, amma ake ci gaba da samun karanci da tsadar fetur a kasar
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Legas - Hukumar kula da tashoshin jiragen ruwa ta ce jiragen ruwa dauke da jimillar lita miliyan 101.9 na man fetur sun iso Najeriya.
Hukumar ta sanar da cewa manyan jiragen za su sauke man fetur din ne a tashar ruwan Apapa da ke Legas a yau ranar Laraba.
Jirage makare da kaya sun iso Najeriya
Hukumar NPA ta ce jiragen ruwa 10 dauke da kayayyaki daban-daban ake sa ran isarsu tashar jiragin ruwan daga 3 zuwa 20 ga watan Nuwamba, inji rahoton Punch.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ta kara da cewa, daga cikin jiragen guda 10, guda uku za su zo da kwantena, daya zai zo da kaya na gama-gari, daya dauke da alkama, daya dauke da gypsum, da wasu dauke da fetur.
Haka zalika, hukumar ta ce jirage uku da za su sauke kaya a tashar ruwa ta Tincan Island daga Litinin zuwa Juma'a na dauke da lita miliyan 58.8 na mai.
An shigo da fetur mai yawa a Najeriya
Jirage 10 ne ake sa ran za su sauke kaya a tashar daga 4 ga Nuwamba zuwa 8 ga Nuwamba, a cewar rahoton na hukumar NPA.
Ya bayyana cewa, ana sa ran jiragen ruwa guda uku dauke da jimillar motoci 1,200 da aka yi amfani da su za su sauke kaya daga 4 zuwa 8 ga watan Nuwamba.
“Wani jirgin ruwa dauke da lita miliyan 20.115 na fetur ya sauka a ranar Talata a tashar Kirikiri Lighter Phase 3a. Wasu jirage biyu dauke da kwantena sun sauka a ranar Litinin."
- A cewar hukumar.
Dangote ya magantu kan shigo da fetur
A wani labarin, mun ruwaito cewa Dangote ya yi martani ga wasu 'yan kasuwa da suka yi ikirarin cewa shigo da fetur ya fi arha fiye da wanda ake samowa daga matatarsa.
Matatar Dangote ta bayyana cewa ta fara siyar da fetur a kan Naira 960 ga masu jiragen ruwa yayin da take sayarwa masu manyan motoci a kan farashin N990.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng