Wani Bom Ya Tarwatse da Mutane a Babbar Kasuwa a Najeriya, An Rasa Rayuka
- Rahotanni sun nuna cewa wani bom da miyagu suka dasa ya tarwatse a kasuwar Orlu da ke jihar Imo a Kudu maso Yamma
- Jami'in hulɗa da jama'an na rundunar ƴan sandan jihar, Henry Okoye ya ce bom din ya tashi da masu ƙokarin dasa shi kuma sun mutu
- Wata majiya ta ce mutane sun shiga tashin hankali bayan fashewar kuma akwai yiwuwar an rasa rayuka
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Imo - Mutane sun shiga tashin hankali a kasuwar Orlu ta ƙasa da ƙasa da ke jihar Imo a lokacin da wani bom da aka dasa ya tarwatse yau Talata.
Rahotanni sun nuna cewa tashin bom din ya yi ajalin mutum biyu a kasuwar da ke Kudu maso gabashin Najeriya.
Yadda tashin bom ya hargiza ƴan kasuwa
Fashewar bom ɗin ta haifar da turmutsutsu, inda jama'a suka fara gudun neman tsira wanda hakan ya sa da dama suka ji rauni, kamar yadda The Nation ta kawo.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wani mutumi da ya nemi a sakaya sunansa ya ce yana kasuwar lokacin da lamarin ya faru, mutane sun tsorata sosai, wasu sun fita hayyacinsu.
"Muna cikin kasuwar lokacin da muka ji ƙarar fashewar wani abu, an shiga tashin hankali da mutane suka fara gudun neman tsira, wasu sun mutu a tashin bom din," in ji shi.
An raya rayuka a tashin bom?
Jami'in hulɗa da jama'a na rundunar ƴan sandan Imo, Henry Okoye, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce ƴan bindiga biyu sun bakunci lahira.
Kakakin ƴan sanda ya ce:
"Bom ne ya fashe kuma tuni kwamishinan ƴan sanda ya tura jami'an sashin kwance bom zuwa wurin. Mutum biyu da ake tunanin su suka sa bom din sun mutu a wurin."
Okoye ya bukaci mazauna yankin su kwantar da hankulansu domin rundunar ta tura ƙarin dakarun ƴan sanda domin dakile duk wata barazana.
Yan sanda sun daƙile hari a Imo
Kuna da labarin jami'an rundunar ƴan sanda na reshen jihar Imo sun samu nasara a yaƙin da suke yi da ƴan ta'adda masu tayar da ƙayar baya.
Ƴan sanda sun daƙile wani harin ƴan ta'adda da ake zargin na ƙungiyar IPOB/ESN ne a ranar Talata, 29 ga watan Oktoban 2024.
Asali: Legit.ng