An Shiga Tashin Hankali, Jami'in NSCDC Ya Mutu a Ban Ɗaki bayan 'Karɓar Albashi'
- Wani mummunan al'amari ya faru a ofishin hukumar NSCDC reshen Iwo, jihar Osun inda aka gano gawar wani jami'i a ban daki
- An rahoto cewa jami'in mai suna Muhammed Opatola ya yanke jiki ya fadi matacce a cikin ban dakin a ranar Litinin
- Yayin da aka yi jana'izarsa a ranar Talata, hukumar NSCDC ta karyata ikirarin cewa zabtare albashi ne silar mutuwar jami'in
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Osun - Al'ummar garin Oyo sun shiga cikin tashin hankali yayin da wani jami'in hukumar tsaron farar hula (NSCDC) ya mutu a cikin makewayi.
An ce jami'in, Muhammed Opatola ya mutu ne a ban dakin ofishin hukumar na Iwo, jihar Osun kuma an birne shi a makabartar Musulmi ta Owoeba, Osogbo.
Jami'in NSCDC ya mutu a makewayi
Kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito, an yi jana'izar jami'in ne a ranar Talata, awanni bayan da aka tsinci gawarsa a cikin bayan gidan.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An rahoto cewa Muhammed Opatola ya yanke jiki ya fadi a makewayin ofishin hukumar NSCDC a ranar Litinin, inda aka tabbatar da mutuwarsa a wani asibiti a Iwo.
Wata majiya da ta nemi a sakaya sunanta, ta ce Opatola ya shiga halin kaka-ni-kayi bayan da ya ga an zabtare wani kaso a albashinsa na wata-wata, inji rahoton The Nation.
Abin da ake zargin ya kashe jami'in
Majiyar ta shaida cewa:
"Jami’in ya yanke jiki ya mutu bayan ya karbi albashin watan Oktoba saboda kudin da yake sa rai ba su ne aka tura masa ba, ya gano cewa an zabtare albashin."
Da aka tuntubi jami’in hulda da jama’a na NSCDC na kasa, Babawale Afolabi ya tabbatar da mutuwar Opatola a wata tattaunawa ta wayar tarho ranar Talata.
Sai dai ya musanta ikirarin cewa jami’in na NSCDC ya mutu ne sakamakon albashin da ya karba yana mai jaddada cewa an tsinci gawarsa a bandaki.
Kotu ta daure jami'in NSCDC a kurkuku
A wani labarin, mun ruwaito cewa wata babbar kotun jihar Katsina ta daure kwamandan hukumar NSCDC shekaru biyar bayan kama shi da laifin cin hanci da rashawa.
Hukumar yaki da cin hanci da rashawa (ICPC) ce ta gurfanar da kwamandan NSCDC, Christopher Oluchukwu bisa zargin ya ci kudin wasu mutane a badakalar daukar aiki.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng