Bayan Hukuncin Kotu, An Bayyana Dalilin Tinubu na Sakin Yaran Kano da Aka Kama
- Sanata Kashim Shettima ya bayyana cewa tausayi da jin kai ya sa Bola Tinubu ba da umarnin a saki yaran Kano da aka tsare
- An ji cewa Tinubu a matsayinsa na uba ƙasa, ya bai wa yaran damar su shiryu su zama na kirki duk da akwai hujjoji a kansu
- Sanata Shettima ya faɗi haka ne yayin da ya karɓi bakuncin yaran a Aso Villa jim kaɗan bayan kotu ta sake su yau Talata a Abuja
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
State House, Abuja - Mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima ya ce Bola Tinubu ya ba da umarnin sakin kananan yaran da aka kama saboda tausayi.
Shettima ya bayyana haka ne a lokacin da ya karbi bakuncin yaran a fadar shugaban ƙasa ranar Talata, 5 ga watan Oktoba, 2024.
Kotu ta sakin yara masu zanga zanga
The Nation ta ce yaran sun ziyarci fadar shugaban ƙasa ne bayan Antoni Janar kuma ministan shari'a, Lateef Fagbemi ya janye duk wata tuhuma a kansu kuma kotu ta sake su.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Idan ba ku manta ba jami'an tsaro sun kama kananan yaran a Kano lokaci zanga-zangar #EndBadGovernance bisa zarginsu da cin amanar ƙasa.
Da yake jawabi yayin da ya karɓi bakuncinsu, Shettima ya ce akwai faifan bidiyon da ya nuna abubuwan da masu zanga-zangar suka aikata da ya saɓa doka.
Dalilin Tinubu na sakin yaran Kano
"Shugaban kasa kuma babban kwamandan rundunar sojin Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, ya bada umarnin sakin yaran ake zargin bisa dalilan jin kai da tausayi.
"Ya sa a sake su duk da akwai kwararan hujjoji na faifan bidiyo da hotunan laifin da suka aikata, kuma da kansu suka wallafa hujjojin."
"Shugaban kasa a matsayinsa na uban kasa ya ƙara ba waɗannan matasan yara damar zama na kirki masu kishin ƙasa da za su ba da gudummuwa wajen gina Najeriya.
- Ƙashim Shettima.
Shettima ya faɗi asarar da zanga-zanga ta jawo
A wani labarin, kun ji cewa mataimakin shugaban ƙasa ya koka kan asarar da aka tafka sakamakon zanga-zangar #EndBadGovernance a watan Agusta.
Kashim Shettima ya bayyana cewa an yi asarar sama da N300bn sakamakon zanga-zangar wacce aka gudanar a faɗin ƙasar nan.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng