Janar Lagbaja na cigaba da Jinya, Tinubu Ya Karawa Mukaddashin Hafsan Sojoji Girma
- Mukaddashin hafsan sojojin Najeriya, Olufemi Oluyede ya samu karin girma zuwa matsayin Laftanar-janar a soja
- Kafin karin girman, Oluyede yana rike da matsayin Manjo-janar ne lokacin da aka naɗa shi mukaddashin hafsan sojoji
- Shugaba Bola Tinubu ne ya karawa Oluyede girma a yau Talata 5 ga watan Nuwambar 2024 a ofishinsa da ke Abuja
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
FCT, Abuja - Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya karawa mukaddashin hafsan sojojin Najeriya girma.
Tinubu ya amince da karin girman zuwa Laftanar-janar Olufemi Oluyede a yau Talata 5 ga watan Nuwambar 2024.
Jinyar Lagbaja ya jawo surutu a Najeriya
Punch ta ruwaito cewa Tinubu ya yi karin girman ne a yau Talata a ofishnsa da ke fadar shugaban kasa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An nada Oluyede mukaddashin hafsan sojojin a madadin Laftanar-janar Taoreed Lagbaja da yake jinya a ketare.
Rashin ganin Lagbaja na tsawon lokaci ya fara sanya shakku a zukatan al'umma kan ainihin abin da ke faruwa.
Wasu rahotanni har sun bayyana cewa ya rasu yayin da yake jinya a ketare kan cutar daji.
Sai dai rundunar tsaro ta musanta labarin inda ya ce kawai Lagbaja ya tafi hutu ne na wadansu makwanni.
Tinubu ya karawa mukaddashin hafsan sojoji girma
Kafin karin girman, Oluyede yana rike da mukamin Manjo-janar ne a gidan soja lokacin da aka naɗa shi mukaddashin hafsan sojoji, cewar BusinessDay.
Tinubu ya yabawa jami'an tsaro kan irin dogewarsu a yaki da ta'addanci, ya ce zai cigaba da ba su goyon baya dari bisa dari.
Sabon mukaddashin hafsan sojoji ya kama aiki
A baya, kun ji cewa Muƙaddashin shugaban rundunar sojojin kasa ta Najeriya da Bola Tinubu ya naɗa ya kama aiki a ofishinsa da ke Abuja ranar Jumu'a.
Manjo Janar Olufemi Oluyede zai riƙe kujerar COAS gabanin dawowar Laftanar Janar Taoreed Lagbaja wanda ya tafi hutun rashin lafiya.
Babban hafsan hafsoshin tsaro CDS, Christopher Musa ya miƙa tutar sojoji ga muƙaddashin hafsun sojojin kasar a hedkwatar tsaro.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng