Najeriya Ta Sake Fadawa Duhu, Tashar Wutar Lantarki Ta Durkushe Karo na 10 a 2024
- Najeriya ta sake fadawa cikin duhu yayin da aka rahoto cewa tashar wutar lantarki ta durkushe a ranar Talata, 5 ga Nuwamba
- An rahoto cewa tashar wutar ta durkushe ne da misalin karfe 2:35 na rana, inda kamfanonin wutar lantarkin suka rasa wutar rabawa
- Durkushewar da tashar wutar ta yi a yau Talata dai shi ne karo na 10 da a cikin shekarar 2024, kwanaki bayan dawo da wuta a Arewa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - A ranar Talata ne tashar da ke samar da wutar lantarki ta Najeriya ta sake fuskantar matsala, lamarin da ya sake jefa kasar cikin wani yanayi na duhu.
Durkushewar tashar wutar lantarkin na yau Talata, shi ne na 10 a cikin wannan shekarar ta 2024, kuma yana zuwa ne a yayin da ake fafutukar gyara wutar Arewa.
Tashar wutar lantarki ta sake durkushewa
The Guardian ta ba da rahoton cewa sabon lamarin, a cewar The Energy Time Podcast, ya faru ne a daidai karfe 2:35 na ranar Talata, 5 ga Nuwambar 2024.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Tashar wutar ta fuskanci rugujewa da dama a cikin watan Oktoba, inda gwamnatin tarayya ta yi alkawarin magance wannan abin kunya na dindindin.
Da misalin karfe 2:35 na rana, alkaluman wutar na sa’o’i ya nuna cewa babu wani kamfanin samar da wutar lantarki da ke da 'megawatt' ko guda daya, inji rahoton Daily Trust.
Mutane sun yi martani kan dauke wutar lantarki
Wani mai sana'ar sayar da kifi, Abdullahi Lawan da muka zanta da shi, ya ce ya tafka asarar Naira N650,000 a rashin wutar da aka samu ta kwanaki.
Abdullahi Lawan wanda ke sana'arsa a Rigasa, Kaduna ya ce yana da kifi a cikin firij, amma sakamakon rashin wutar lantarkin ya sa suka lalace.
Yayin da Malam Abdullahi ya ke wannan korafi, Haji Sufi da ke sana'ar cajin waya a layin Magaji, titin Makarfi, Rigasa Kaduna, ya ce ya samu arziki ta dalilin daukewar wutar.
Haji Sufi ya ce kafin tashar wutar ta rika lalacewa, kwastomominsa ba sa wuce 20 a rana, amma bayan dauke wutar, yana caja waya sama da 100 a kowace rana.
Martanin jama'a daga soshiyal midiya
Jim kadan da samun labarin daukewar wutar lantarkin, wasu daga cikin 'yan Najeriya sun bayyana ra'ayoyinsu mabambanta a shafukan sada zumunta.
Sadik Isa:
"InnalilLahi wa inna iLaihi raji'un, gaskiya wannan lamari akwai sa hannun wasu 'yan iska a cikin shi."
Muhammadu Yahya:
"Duk wanda ya san ya yi wa mai cajin unguwar su rashin kunya da wuta da dawo yaje ya ba shi hakuri tun dare bai yi masa ba."
Haris Maikasa:
"Idan ba Allah ne ya kiyaye ba wannan matsalar ita za ta kawo karshen masu garkuwa da mutane domin ita kuma ta samu gurin zama. Allah ya kawo mana mafuta."
Naziru Hamisu Usman:
"Nifa ina ganin wannan abin ba zai rasa nasaba da son raba Nigeria ba. Ana ta kara kudin mai ana son 'yan Arewa su yi bore."
TCN ta na kokarin gyara tashar wuta
A wani labarin, mun ruwaito cewa gwamnatin tarayya ta ce ana ci gaba da aikin gyara tashar wutar lantarkin kasar da ta lalace a ranar Litinin, 14 ga watan Oktoba.
A wata sanarwa da ta fitar a ranar Talata 15 ga Oktoba, manajan hulda da jama’a na TCN, Ndidi Mbah, ya ce an kusa kammala gyaran tashar wutar lantarkin.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng