Zanga Zanga: Kashim Shettima Zai Tarbi Yara bayan Gwamnati Ta Janye Shari'a a Kotu

Zanga Zanga: Kashim Shettima Zai Tarbi Yara bayan Gwamnati Ta Janye Shari'a a Kotu

  • Yaran da gwamnati ta janye shari’a da su za su shiga fadar shugaban kasar nan watau Aso Rock a babban birnin tarayya Abuja
  • Wannan na zuwa bayan kotu ta kori karar da gwamnatin Bola Tinubu ta shigar a gabanta na zargin yaran da cin amanar kasa
  • Gwamnatin tarayya ta dakatar da shari’a da ta ke yi da mutane akalla 119, daga cikinsu har da kananan yara saboda zanga zanga

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT AbujaYaran da gwamnatin kasar nan ta gurfanar a gaban kotu bisa zargin cin amanar kasa za su shiga fadar Aso Rock da ke Abuja.

Kara karanta wannan

Sanatocin Arewa sun fadi dalilin Tinubu na sakin kananan yaran da aka kama

Mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima ne zai karbi bakuncin yaran bayan kotu ta sallame su a yau Talata, tare da soke tuhumar kokarin kifar da gwamnati da aka yi masu.

Kashim
Yaran da gwamnati ta daina sharia da su za su shiga Aso Rock Hoto: Kashim Shettima/Sanusi Bature Dawakin Tofa
Asali: Facebook

Jaridar The Cable ta wallafa cewa an saki yaran ne bayan shugaban kasa Tinubu ya umarci babban lauyan kasa, Lateef Fagbemi da a janye tuhumar da ake yi masu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Dalilin da ya sa gwamnatin Tinubu ta saki yara

Gwamnatin tarayya ta bayar da umarnin sakin kananan yaran da ta gurfanar a gaban kotu bayan sun fito a watan Agusta domin gudanar da zanga zangar adawa da matsin rayuwa.

A lokacin da aka aka gurfanar da yaran a gaban kotu, an gano su da alamun yunwa, wanda ya fusata yan kasa da su ka matsawa gwamnati ta soke tuhumar da ta ke yi masu.

Kara karanta wannan

Za a zaƙulo yan sandan da suka 'azabtar' da yara masu zanga zanga Inji IGP

Gwamnatin tarayya za ta tarbi yaran Kano

An jima kadan ake sa ran gwamnatin tarayya za ta mika yaran ga wakilan gwambatin jihar Kano domin dawo da yaran gaban iyayensu.

Yaran sun samu shakar iskar yanci ne bayan an samu yan kasar nan sun yi kururuwar neman gwamnatin tarayya ta jingine tuhumar da ta ke yi masu..

Kotu ta karbi bukatar lauyan gwamnati

A baya kun ji cewa a yau Talata ne babbar kotun tarayya Abuja ta kori karar da gwamnatin Tinubu ta shigar gabanta na tuhumar mutane akalla 119 saboda shiga zanga zangar.

An saki yaran ne bayan shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya bayar da umarnin a janye tuhumar cin amanar kasa da kokarin kifar da gwamnatinsa da daga tutar Rasha.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.