Sojoji Sun Saki Bom kan Jagoran Yan Ta'adda, An Kashe Miyagu 50

Sojoji Sun Saki Bom kan Jagoran Yan Ta'adda, An Kashe Miyagu 50

  • Rundunar sojin saman Nigeriya ta yi luguden wuta kan yan ta'addar ISWAP a jihar Borno da ke Arewa maso Gabashin Najeriya
  • Rahotanni sun nuna cewa sojojin saman Najeriya sun saki wuta ne a wata maboyar yan ta'addar a karamar hukumar Marte
  • Kai farmakin da sojojin suka yi ya jawo kashe wani jagoran yan ta'addar ISWAP mai suna Bashir Dauda da tarin miyagu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Borno - Sojojin Najeriya sun yi wani luguden wuta a kan yan ta'addar ISWAP masu yawa a jihar Borno.

Rahotanni na nuni da cewa sojojin sun samu nasarar hallaka yan ta'addar ISWAP kimanin 50 yayin luguden wutar.

Kara karanta wannan

Sojojin sama sun yi ajalin 'yan ta'adda da ke kokarin hana gyara lantarkin Arewa

sojoji
Sojojin Najeriya sun kashe jagoran ISWAP. Hoto: Nigerian Air Force HQ
Asali: Getty Images

Jaridar the Nation ta wallafa cewa kakakin sojojin saman Najeriya, Olusola Akinboyewa ne ya sanar da lamarin ga manema labarai.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An kashe jagoran yan ta'addar ISWAP

Rundunar sojin saman Nigeriya ta kashe wani babban jagoran yan ta'addar kungiyar ISWAP, Bashir Dauda a jihar Borno.

Rahotanni sun nuna cewa sojojin sun kashe Bashir Dauda bayan luguden wuta da suka yi a karamar hukumar Marte.

An kashe yan ISWAP a Borno

Bayan kisan jagoran yan ta'addar, sojin saman Nigeriya sun samu nasarar kashe ƙarin yan ta'addar kungiyar ISWAP 49.

Sojojin sannan Najeriya sun kashe yan ta'addar ne a wasu wurare hudu da aka yi wa luguden wuta a kokarin yaki da ta'addanci a Arewa maso Gabas.

Sojoji sun lalata abincin ISWAP

Daga cikin nasarar da sojojin suka samu akwai lalata kayan abincin yan ta'addar a yankunan Jubalaram, Buluwa da Tumbu Karfe.

Kara karanta wannan

Ana rigimar tsare yara 72, jami'an tsaro sun harbi daraktan fina finai a tumbi

Sojojin sun yi nasarar lalata shinkafa, gero da wake na yan ta'addar wanda hakan zai iya jefa miyagun cikin rashin abinci.

Olusola Akinboyewa ya ce hakan na cikin ƙoƙarin da sojojin saman Najeriya ke yi wajen ba da gudunmawa a kan yaki da miyagu.

An ceto matafiya 19 a jihar Neja

A wani rahoton, mun ruwaito muku cewa yan sandan Najeriya a jihar Neja sun yi nasarar ceto mutane 19 da aka sace.

Rahotanni sun nuna cewa an sace mutane 19 ne yayin da suka fito daga jihar Sokoto za su yi tafiya zuwa jihar Bayelsa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng