Yan Sanda Sun Yi Gumurzu da Yan Bindiga a Daji, An Ceto Matafiya
- Rundunar yan sandan jihar Neja ta tabbatar da cewa ta ceto wasu mutane da yan bindiga masu garkuwa da mutane suka sace
- Rahotanni sun nuna cewa mutanen da aka ceto din an sace su ne yayin da suka dauko hanya zuwa Bayelsa daga jihar Sokoto
- A ranar 1 ga watan Nuwamba ne yan bindiga suka sace matafiyan a wata mota kirar Toyota a kan hanyar Tegina zuwa Zungeru
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Niger - Rundunar yan sanda a jihar Neja ta tabbatar da ceto wasu mutane kusan 20 da yan bindiga suka yi garkuwa da su.
Tun a ranar Juma'a, 1 ga Nuwamba yan bindiga suka sace mutanen a kan hanya suka shiga da su cikin wani daji.
Jaridar Punch ta wallafa cewa kakakin yan sanda a jihar Neja, Wasiu Abiodun ya tabbatar da ceto mutanen daga hannun yan bindiga.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
'Yan bindiga sun sace matafiya a jihar Neja
Tun a ranar Juma'a, 1 ga Nuwamba a jihar Neja wasu 'yan bindiga sun kama matafiya za su nufi Bayelsa
Yan bindigar sun kama matafiya 19 kuma suka nufi jeji da su a karamar hukumar Rafi ta jihar Neja.
Yan sanda sun ceto matafiya a Neja
Kakakin yan sanda, Wasiu Abiodun ya bayyana cewa tun da aka sace matafiyan jami'ansu suka fara yunkurin ceto su.
Rahoton Channels Television ya nuna cewa a ranar 2 ga Nuwamba yan sanda suka fafata da miyagun inda suka ceto mutane 12 cikin matafiyan.
A yammacin ranar yan sanda suka kara shiri suka nufi dajin da yan ta'addar suke kuma sun samu nasarar ceto sauran mutane bakwai din.
An kai matafiya da aka sace asibiti
Rundunar yan sanda ta tabbatar da cewa ta mika matafiyan da aka ceto zuwa asibiti domin karɓar kulawa.
Bayan sun samu sauki, yan sanda sun mika su ga yan uwansu a jihar Sokoto kamar yadda Wasiu Abiodun ya tabbatar.
Sojoji sun hallaka yan ta'adda
A wani rahoton, kun ji cewa sojojin saman Najeriya sun samu nasarar dakile sabon hari da yan bindiga za su kai kan layukan wutar lantarkin Arewa.
Kakakin rundunar sojojin sama a kasar nan, 'Air Commodore' Olusola Akinboyewa ne ya bayyana nasarar da su ka samu a sanarwar da ya fitar.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng