Wani Jirgi da Ya Nufi Abuja Ya Samu Matsala a Sama, Bayanai Sun Fito

Wani Jirgi da Ya Nufi Abuja Ya Samu Matsala a Sama, Bayanai Sun Fito

  • Kamfanin jigilar jiragen saman Air Peace ya bayyana cewa jirgin da ya dauko fasinjoji daga Edo zuwa Abuja ya samu matsala ana tafiya
  • Kakakin kamfanin Air Peace, Ejike Ndulio ya tabbatar da cewa a yanzu haka injiniyoyi na kokarin shawo kan matsalolin da suka faru
  • Ejike Ndulio ya kuma tabbatar da cewa za su cigaba da ƙoƙarin tabbatar da tsari mai kyau domin kiyaye lafiyar matafiya a Najeriya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Edo - Jirgin saman kamfanin Air Peace da ya dauko mutane daga Benin zuwa Abuja ya samu matsala a sararin samaniya.

Kamfanin Air Peace ya tabbatar da faruwar lamarin kuma ya bayyana halin da fasinjoji suka shiga.

Kara karanta wannan

Bayan masifar yan bindiga, wasu gungun miyagu daban sun sake bulla a Sokoto

Jirgi
Jirgi ya koma Edo bayan samun matsala a sama. Hoto: Air Peace
Asali: Facebook

Legit ta tatttaro bayanai kan abin da ya faru ne a cikin wani sako da kamfanin Air Peace ya wallafa a shafinsa na Facebook.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Jirgin ya samu matsala a sama

Kamfanin jigilar jiragen saman Air Peace ya tabbatar da cewa wani jirginsa da ya dauko mutane ya samu matsala.

Kakakin kamfanin Air Peace, Ejike Ndulio ya tabbatar da cewa jirgin ya dauko mutane ne daga Benin zuwa birnin tarayya Abuja.

Yadda jirgi ya koma Benin saboda tangarda

Biyo bayan matsalar da jirgin ya samu, ya yi saukar gaggawa yayin da ya koma birnin Benin na jihar Edo.

Kamfanin Air Peace ya tabbatar da cewa ya dauki matakin ne domin tabbatar da kare rayukan mutanen da aka ɗauko.

Punch ta wallafa cewa jirgin ya sauka lafiya a Benin kuma fasinjoji sun cigaba da harkokinsu yayin da ake gyara matsalar da ta faru.

Kara karanta wannan

Matsafi ya kashe mata 76 ya cinye namansu, ya fadi alaƙarsa da 'yan siyasa

Jirgin Air Peace ya ba mutane hakuri

Kamfanin Air Peace ya ba al'umma hakuri kan abin da ya faru musamman wadanda za su samu tsaiko saboda matsalar da aka samu.

Air Peace ya tabbatar da cewa zai cigaba da kokari wajen tabbatar da lamura da suka shafi zirga-zirga suna tafiya daidai.

Ana zakulo wadanda hadarin jirgi ya ritsa

A wani rahoton, kun ji cewa ofishin NSIB ya tabbatar da cigaba da aikin zakulo gawargwakin wadanda su ka mutu a hadarin jirgin sama.

Wani jirgi mai saukar ungulu da kamfanin mai na kasa (NNPCL) ya dauko haya ya fadi a garin Fatakwal da ke jihar Ribas a watan da ya wuce.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng