Sojojin Sama Sun Yi Ajalin Yan Bindiga da ke Kokarin Hana Gyara Lantarkin Arewa

Sojojin Sama Sun Yi Ajalin Yan Bindiga da ke Kokarin Hana Gyara Lantarkin Arewa

  • Rundunar sojojin saman Najeriya ta ce an samu nasarar dakile sabon hari da yan bindiga za su kai kan layukan wutar lantarkin Arewa
  • Kakakin rundunar sojojin sama a kasar nan, 'Air Commodore' Olusola Akinboyewa ne ya bayyana nasarar da su ka samu a sanarwar da ya fitar
  • Olusola Akinboyewa ya shaida cewa dakarun sun samu labarin yan bindiga za su kai farmaki kan injiniyoyin da ke gyaran lantarki

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kaduna – Rundunar sojojin saman Najeriya ta yi luguden wuta a kan wasu yan bindiga da su ka yi yunkurin hana gyara layukan wuta da ke kawo haske ga Arewa.

Kara karanta wannan

Band A: Masu samun wutar awa 20 a rana sun gaji, sun kai kuka wajen Tinubu

An kashe yan ta’addan da dama a lokacin da dakarun sojin sama ke ba masu gyara babban layin lantarkin da ke dauko lantarki daga babbar Tashar Shiroro zuwa Kaduna kariya.

Transmission Company of Nigeria
An kashe yan bindiga masu lalata turakun lantarki Hoto: Transmission Company of Nigeria
Asali: Facebook

Jaridar Daily Trust ta wallafa cewa an samu rahotannin yan bindigar na kokarin kara lalata layukan lantarki a lokacin da su ka gamu da ajalinsu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Dakarun Sojojin sama sun kashe yan ta’adda

Jaridar Aminiya ta ruwaito cewa dakarun sojojin saman kasar nan sun kashe yan ta’adda da dama a ranar Juma’a da ta gabata.

An hango yan ta’addan a hanyarsu ta kara lalata turakun lantarki da su ka lalata a baya har ya haddasa rashin wuta a jihohin Arewacin Najeriya akalla 17.

Sojojin sama sun kare harin yan ta’adda

Kakakin rundunar sojojin sama ta kasa, Olusola Akinboyewa ya bayyana cewa jami’ansu sun dakile kai hari kan ma’aikatan da ke gyara layin latarki a Arewa.

Kara karanta wannan

Ba a gama da Kano ba, gwamnatin Zulum ta gurfanar da kananan yara da wasu 16

Sojojin na daga cikin wadanda aka ba aikin bayar da kariya ga injiniyoyin kamfanin hasken wutar lantarki na kasa (TCN) da ke kokarin gyara layukan wuta da yan bindiga su ka lalata.

“Yan bindiga sun hana gyara lantarki:” TCN

A baya mun ruwaito cewa kamfanin hasken wutar lantarki na kasa (TCN) ya dora alhakin jinkirin da aka samu wajen gyara wutar lantarki da ta lalace a Arewa a kan yan bindiga.

Shugaban TCN, Injiniya Sule Ahmed Abdulaziz ya bayyana cewa injiniyoyinsu na cikin tsaka mai wuya inda su ke fama da yan bindiga a wajen gyaran turakan wuta bayan Arewacin kasar nan.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.