Kamfanin MTN Ya Sake Yin Gagarumar Asarar Kudi a Shekarar 2024, An Gano Dalili
- Kamfanin sadarwa na MTN ya bayyana cewa ya yi asarar N514.9bn (bayan an cire haraji) a cikin watanni tara na shekarar 2024
- A rahoton kudi na zango na uku da MTN ya fitar, kamfanin ya ce asarar ta ragu da N4.1bn idan aka kwatanta da zango na biyu
- Yayin daka dora alhakin asarar ga faduwar darajar Naira, MTN ya kuma ce an samu raguwar masu amfani da layukansa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Bayan shafe watanni tara yana gudanar da aiki a cikin shekarar 2024, babban kamfanin sadarwa a Najeriya, MTN, ya fitar da alkaluman hada-hadar kudinsa.
Daga Janairu zuwa Satumbar 2024, kamfanin sadarwa na MTN ya ce ya samu riba yayin da kuma ya tafka asara, bayan tattara rahoton kudin a ranar 30 ga Satumba.
MTN ya yi asarar N514.9bn a 2024
Kamfanin MTN ya ce ya yi asarar N514.9bn (ribar N4.1bn bayan an cire haraji) yayin da aka yi asarar hada hadar kudin waje na N118.5bn inji rahoton Daily Trust.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An yi hasarar ne saboda faduwar darajar Naira inda aka samu ragin N4.1bn a cikin asarar zango na uku idan aka kwatanta da asarar N519.1bn da aka samu a zango na biyu.
Duk da tabarbarewar tattalin arziki, kudin shiga na ayyukan da kamfanin MTN yake yi sun karu da kashi 33.6 zuwa Naira tiriliyan 2.4.
Masu amfani da layin MTN sun ragu
Jimillar masu amfani da MTN ya ragu da 0.9% zuwa miliyan 77 a watannin bayan.
An dora alhakin hakan ga tsarin hada layuka da lambar NIN, wanda ya tilasta kamfanonin sadarwa rufe layuka marasa rajista.
Tribune ta rahoto cewa, masu amfani da 'Data' sun karu da 5.1% zuwa miliyan 45.3 yayin da masu amfani da asusun MoMo PSB suka ragu da 21.8% zuwa miliyan 2.8.
A halin da ake ciki, kamfanin ya ce zai tara N50bn ta hanyar fitar da sabon takardar kasuwanci (CP) a karkashin shirinsa na bayar da takardan kasuwanci na N250bn.
MTN ya yi asarar Naira biliyan 11
Tun da fari, mun ruwaito cewa katsewar sama da wayoyin sadarwa 6,000 a tsakanin shekarar 2022 zuwa 2023 ya jawo kamfanin MTN ya yi asarar Naira biliyan 11.
Rahoton da kamfanin IHS ya nuna cewa kudin da MTN ya kashe sakamakon lalacewar wayoyin ya isa ya gina sababbin wayoyin na kilomita 870 a wuraren da ba sabis.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng