Ana Murna Gwamna a Arewa Ya Fara Biyan Ma'aikata Sabon Albashi na N70,000

Ana Murna Gwamna a Arewa Ya Fara Biyan Ma'aikata Sabon Albashi na N70,000

  • Gwamna Babagana Umaru Zulum ya fara biyan ma'aikata sabon mafi ƙarancin albashi na N70,000 a jihar Borno
  • Shugaban kwamitin albashi kuma kwamishinan kasafi da tsare tsare, ya ce ma'aikata sun fara ganin sabon albashin
  • Ya yabawa Gwamna Zulum bisa goyon bayan da ya bai wa kwamitin wajen ganin ma'aikata sun amfana da sabuwar dokar albashin

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Borno - Gwamnatin jihar Borno karkashin jagorancin Farfesa Babagana Umaru Zulum.ta tabbatar da fara biyan sabon mafi ƙarancin albashi.

Shugaban kwamitin da aka kafa, Dokta Babagana Mallambe, ya ce tuni ma'aikata suka fara ganin sabon albashin a asusun bankunansu.

Gwamna Babagana Zulum.
Gwamnatin Borno ta fara biyan sabon mafi ƙarancin albashi na N70,000 Hoto: Prof. Babagana Umara Zulum
Asali: Facebook

Babagana Mallambe, wanda shi ne kwamishinan kasafi da tsare-tsare na Borno ya faɗi haka da yake hira da manema labarai ranar Litinin, Daily Trust ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Ma'aikata za su fuskanci matsala, za a samu jinkirin albashin wasu watanni

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamna Babagana Zulum ya cika alƙawari

Ya ce gwamnatin Borno ta fara biyan ma'aikata sabon albashin a watan Oktoba ne domin zaburar da su da kuma inganta walwala da jin daɗinsu.

Kwamishinan ya ce dukkanin ma’aikatan gwamnati sun fara karbar mafi karancin albashi tun ranar Juma’ar da ta gabata.

“Ina mai matukar farin cikin sanar da ku cewa an fara biyan sabon mafi karancin albashi na N70,000 ga dukkan nau’o’in ma’aikatan jihar Borno.
"Wannan ba ƙaramar nasara ba ce a jiharmu kuma alama ce da ke nuna yadda Mai girga gwamna Babagana Zulum ya ɗauki ma'aikata da muhimmanci.
"Bari na yi amfani da wannan damar wajen jinjinawa mai girma gwamna bisa dukkan goyon bayan da ya ba da har muka kammala wannan aiki.

Ƴan kwadago sun buƙaci a duba ƙananun ma'aikata

A nasa jawabin shugaban ƙungiyar kwadago NLC na jihar, Kwamared Inuwa ya yabawa gwamnatin Borno bisa gaggauta aiwatar da sabon mafi karancin albashi.

Kara karanta wannan

Gwamna Uba Sani ya amince da sabon mafi karancin albashi ga ma'aikatan Kaduna

Ya kuma yi kira da a faɗaɗa biyan sabon albashin zuwa ƙananan hukumomi 27 na jihar, wanda a cewarsa ba a yi wa ƙananun ma'aikatan ƙarin albashin ba. 

Gwamma zai yi ƙarin albashi a watan zaɓe

A wani rahoton, an ji cewa Gwamna Lucky Aiyedatiwa ya ce gwamnatinsa za ta fara biyan sabon mafi ƙarancin albashi na N73,000 a watan Nuwamba, 2024

A ranar 21 ga watan Nuwamban da muke ciki za a gudanar da zaɓen gwamna a jihar Ondo da Aiyedatiwa ke takara a inuwar APC.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262