Shugaba Tinubu Ya Fadi Nasarar da Ya Samu a Watanni 18 bayan Ya Gaji Buhari
- Bola Ahmed Tinubu ya ce gwamnatinsa ta yi nasarar rage kudin da ake kashewa a wajen biyan basussukan da ake bin Najeriya
- Shugaba Tinubu ya bayyana cewa a lokacin da ya kama ragamar kasar nan, ana amfani da 97% na kudin shiga domin biyan bashi
- Tinubu ya ce a yanzu, kasar nan ta na amfan da 65% na kudin shigarta domin biyan basussukan wanda ke nuna nasara babba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT Abuja – Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya jinjna yadda gwamnatinsa ta yi nasarar rage kudin da ake kashewa a kan basussukan da gwamnatin baya ta laftowa kasar nan.
Shugaban na magana ne a ranar Litinin yayin rantsar da sababbin Ministoci guda bakwai da gwamnatinsa ta nada domin taya shi gudanar da gwamnati.
Jaridar The Cable ta ruwaito Tinubu ya yi ce nasarar da aka samu wajen samun raguwar kudin da kasar nan ta ke kashewa a kan basussukan da ake bin ta ya na kara bunkasa tattalin arzikin kasa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Bola Tinubu ya fadi yadda ya samu Najeriya
Jaridar Daily Trust ta wallafa cewa shugaba Bola Ahmed Tinubu ya ce kason kudin shiga da ake kashewa wajen biyan bashin da ake bin kasar nan ya ragu daga 97% zuwa 65%.
Shugaba Tinubu ya ce a lokacin da ya karbi jagorancin kasar nan daga Muhammadu Buhari, kasar ta na biyan basussuka da akalla 97% na kudin shiga da ta ke samu.
“Tattalin arziki na farfadowa:” Tinubu
Shugaban Najeriya, Bola Tinubu ya ce tun bayan fara mulkinsa zuwa yanzu, ana samun ci gaba a fannin farfado da tattalin arzikin kasa.
Duk da Tinubu ya amince akwai gagarumin kalubale a gaban gwamnati, amma ya na da yakinin kasar nan za ta cimma burinta na cigaba da yara da jikoki za su mora a nan gaba.
Tattalin arziki: Gwamnatin Tinubu ta soki Atiku
A baya kun ji gwamnatin Bola Ahmed Tinubu ta soki tsare-tsaren tattalin arziki da tsohon dan takarar shugaban kasa, Atiku Abubakar ya bayyana cewa za su fi na Tinubu gyara kasa.
A sanarwar da hadimin shugaban, Bayo Onanuga ya fitar, ya ce ‘yan Najeriya ba su gamsu da tsarin da Atiku Abubakar ya zo da su ba, shi ya sa su ka ki zabarsa a zaben 2023.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng