Zanga Zanga Ta Barke a Hedikwatar NNPCL, Mele Kyari Ya Shiga Tsaka Mai Wuya
- Masu zanga-zanga sun cika hedikwatar kamfanin NNPCL a Abuja inda suka bukaci kawo sauyi tattare da harkokin mai
- Matasan da ke zanga-zangar sun bukaci Mele Kyari ya yi gaggawar ajiye aikinsa na shugaban kamfanin NNPCL saboda gazawa
- Hakan ya biyo bayan korafe-korafe kan tashin farashi da yawan layi da ake samu a gidajen mai da kuma halin kunci da aka shiga
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
FCT, Abuja - Matasa masu zanga-zanga sun mamaye hedikwatar kamfanin mai na NNPCL da ke birnin Tarayya Abuja.
Masu zanga-zangar sun bukaci shugaban kamfanin, Mele Kyari ya yi gaggawar yin murabus daga mukaminsa saboda matsalolin da ake samu.
Zanga-zanga ta barke a NNPCL saboda tsadar mai
Matasan sun nuna damuwa kan rashin kwarewar shugabancin Kyari da yawan tashin farashin fetur da layi a gidajen mai, cewar Punch.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Jagoran masu zanga-zangar da suka hada da sauran kungiyoyi, Abdullahi Bilal ya ce Kyari ya gaza a sha'anin shugabancin kamfanin.
Bilal ya ce yawan tashin farashin mai a kasar ya jefa mutane cikin mummunan hali da kuma kangin talauci, The Guardian ta ruwaito.
Matasa sun koka kan gurbataccen mai a kasa
Masu zanga-zangar sun koka kan shigo da gurbataccen mai wanda cin hanci ke jawowa da ke kawo cikas ga ababan hawa.
"A yau muna kiran shugaban kamfanin NNPCL, Mele Kyari ya yi murabus saboda gazawa a bangaren mai a kasar."
"Karkashin jagorancinsa mun fuskanci tsadar mai da yawan layi a gidajen mai da kuma shigo da gurbataccen mai daga ketare."
- Abdullahi Bilal
Bayan NNPCL, yan kasuwa sun kara kudin mai
Kun ji cewa yayin da ƴan Najeriya ke kokawa kan tsadar rayuwa, ƴan kasuwar mai sun ƙara farshin litar man fetur a faɗin ƙasar nan.
Dillalan man sun kara farashin kayansu ne kwanaki ƙalilan bayan kamfanin mai na ƙasa NNPCL ya ƙara farashin litar mai a gidajen mansa.
Rahotanni sun tabbatar cewa manyan ƴan kasuwa sun ƙara farashin litar fetur daga N1,010 zuwa N1,050 a Lagas da yankunan da ke kewaye ta ita.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng